Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin Amurka

Spread the love

Shugaban Amurka Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin Amurka a wa’adin mulki na biyu.

Cikin jawabin da ya yi a wani taron manema labarai, shugaban ya ce ya yi hakan ne domin ”masalahar jam’iyyarsa da kuma ƙasarsa”.

Ya ce cikin shekara uku da rabi da ya yi yana jagorantar Amurka, ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.

”A yau Amurka na da ƙarfin tattalin arziki a duniya, mun kafa tarihi a fannin zuba jari domin sake gina ƙasarmu”.

A baya-bayan nan dai shugaban ya fuskanci matsin lamba daga manyan ‘yan jam’iyyarsa da ke kiraye-kirayen ya haƙura da takara, tun bayan rashin katabus a muhawarsa da Donald Trump.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *