Ka da wata masarauta ta ɓoye makasan sojoji 17 – Gwamnan Delta

Spread the love

Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya gargaɗi sarakunan gargajiya da ke jihar kan bai wa waɗanda ake zargi da kisan sojojin Najeriya 17 mafaka.

Ya bayyana haka ne ranar Alhamis, mako ɗaya da faruwar mummunan lamarin.

An kashe sojojin ne yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umomin yankin Okuama da ba sa ga maciji da juna a ƙaramar hukumar Ughelli da ke jihar ta Delta.

Gwamnan ya bayyana buƙatarsa ta son sarakunan gargajiya su bai wa hukumomi haɗin kai a aikin da suke na gano waɗanda suka kashe dakarun.

Da yake yi wa sarakunan gargajiyar bayani a birnin Asaba, gwamna Oborevwori ya ce Delta tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka inda ya nanata cewa bai kamata wata masarauta ta bai wa mutanen da suka yi taɓargazar kariya ba.

Gwamnan ya ƙara da cewa shugaba Bola Tinubu da sojoji sun ba shi tabbaci cewa ba za a muzgunawa farar hular da ba su ji ba su gani ba yayin binciken.

‘Ba za mu bar Okuama ba har sai an zaƙulo waɗanda suka kashe sojojinmu 17’

Diphtheria Ta Yi Ajalin Yara 4 A Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *