Kaiyade Shekarun Rubuta Jarrabwar WAEC, WASSCE,NECO ,Ba Zai Haifarwa Nigeria Da Mai Ido Ba: Dr. Aliyu Yusuf Ahmed.

Spread the love

Masana harkokin ilimi sun fara yin tsokaci kan matakin gwamnatin tarayya, kan hana duk yaron da bai kai  shekaru 18 da haihuwa , rubuta jarrabawar kammala makarantar sakandire ba.

To sai dai Dr. Aliyu Yusuf Ahmed, malami a jami’ar kimiya da fasaha ta Aliko Dangote dake garin Wudil a jahar Kano, ya bayyana cewa matakin da karan tsaye  kan yancin cin gashin kai da yakamata a ce jami’o’in kasar suna da shi.

Dr. Aliyu  Ahmed, ya kara da cewa yin hakan zai haifar da illa domin kaiyade shekarun yaron da zai je makarantar jami’a sune suka fi kowa yancin su tsayar da shekarun da suke bukata.

A ranar Litinin 26 ga watan Augusta 2024, ministan ilimin Najeriya, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa babu yaron da za a sake bari ya zauna jarrabawar kammala sakandire ba tare da cika shekaru 18 da haihuwa ba.

Farfesan wanda ya bayyana hakan yayin wata hira a shirin “Sunday Politics” ranar Lahadi na gidan talbijin na Channels, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin da ke kula da zana jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da WASSCE da NECO da su bi sabon umarnin nata na kasancewar yara ƴan shekara 18 kafin cancantar zama a jarrabawar.

A cewar Dr. Aliyu Yusuf Ahmed, shekaru suna bayar da tasiri akan karatun yaro, kuma akasari shekarun da akan dauka domin shiga makarantun Primary shi ne shekaru 6, kuma a mafi yawan kasashen duniya haka yake.

‘’  kuma in ka dauka yaro zai yi  karatu na shekara 6 a Primary sannan ya yi sheakru 6 a makarantar sakandire idan ka hada zai kai shekaru 18 kafin ace yaro ya shiga jami’a’’ cewar Dr. Aliyu Yusuf Ahmed’’.

Ya ce sau da yawa sauya wannan lokaci na karatu a ilimance yana iya haifar wa da wasu yara matsala, domin bincike ya nuna cewa idan ka kai yaro dan shekaru uku ka hada shi da yan shekaru 6 a makarantar primary bincike da yawa ya nuna cewar idan aka yi rashin sa’a yaro yana iya samun rashin karsashi na karatu kodan saboda kankantarsa ko kuma tsangwama da daidai sauransu.

‘’ amma matsalar shi ne anan an yi wa yara kudin Goro, domin sau dayawa a wannan kasa ta mu an samu,  a duniya an samu yara ma su karancin shekaru sun samu baiwa ta ilimi wanda akwai tasgaro ga wanda Allah ya yi baiwa ace dole sai an cire shi daga matsayin da Alllah ya dora shi’’

An samu irin yaran nan da yawa domin akwai yaro dan shekaru 11 a kasar India wanda wata makaranta ta bashi Professsor,

Saboda girman ilimansa, haka ma kasashe da dama an samu yara wadanda suka kai farfesoshi da suka yi karatu na daya har zuwa na uku a cikin shekaru 19 kachal.

Dr. Aliyu ya ce bai kamata Nigeria ta yanke wa kan irin wannan hukuncin cewar ba zata taba samun yara masu baiwar da za a hada su aji da manya kuma su fahimci karatun.

Ya bayar da shawarwarin da yakamata gwamnatin tarayyar ta dauka , ta guji yin karan tsaye ga jami’o’I domin hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Sai dai ya ce abaya yan majalissun dattawa sun bayyana cewa lallai dokokin Nigeria kafin a sauya su  lallai sai an zauna da ma su ruwa da tsaki.

‘’ a matsayi na malami a jami’a, domin ina cikin kungiyar ASUU,  kuma a wani bangaren ina cikin ma su ruwa da tsaki, zan ce lallai gwamnati bata zauna da masu ruwa tsaki don tattauna wannan lamari ba wanda kuma yana da kyau ta kalle su da idon basira’’.

Muryar Dr. Aliyu Yusuf Ahmed

‘’ cikin hujja da suka kafa na yin wannan kasancewar yara masu karancin shekaru sun shiga jami’a kuma hakan yana haifarwa da jami’a illoli a bisa fahimtarsu’’ Dr. Aliyu Yusuf Ahemd’’.

‘’amma indai an bi daukar karatun jami’a  bisa tsari, ita wannan jarrabawa tana tafiya akan cancanta ba mutane suna bin wasu hanyoyi ta bayan gida ba zaka samu masu cin jarrabawar suna kaiwa shekaru 18, sai kalilan da masu baiwa wadanda ba su kai shekarun ba su tsallake su shiga jami’ar’’

Ministan ya kuma ƙara da cewa sabuwar ƙa’idar ta shafi yaran da ke son zauna jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare da ake kira UTME da hukumar JAMB ke tsarawa.

“Abin da muka yi a taron da muka yi da hukumar JAMB a watan Yuli shi ne mu fara aiwatar da wannan sabuwar dokar a shekarar 2025 domin bai wa iyayen yara isasshen lokacin shiri. Hukumar ta JAMB za ta tabbatar da cewa duk yaron da zai nemi gurbin shiga jami’a dole ne sai ya cika sharuɗɗan ƙasar na kasancewar ɗan shekara 18,” in ji ministan.

“Kuma ai idan kuka ƙirga shekarun da ya kamata yaro ya kammala sakandare tunda daga shigarsa nazare zuwa firamare zuwa ƙaramar sakandare har ya kammala babbar sakandare, za su kasance 17 da rabi. Za su ƙarasa 18 lokacin da za su samu gurbin shiga jami’a,” kamar yadda ministan ya ƙara.

Ministan ya yi ƙarin haske dangane da shekarun da ya kamata kowanne yaro ya kwashe a makarantun kafin firamare da na firamare har zuwa kammala sakandare.

“Ya kamata yaro ya kwashe shekaru biyar na farko a makarantun nazare. Sannan a shekara shida ya kamata yaro ya fara makarantar firamare, inda kuma zai kwashe shekaru shida a firamare ɗin sannan ya wuce ƙaramar sakandare a shekaru 12 inda zai yi shekaru uku. Daga nan sai ya shiga babbar sakandare a 15, inda nan ma zai kwashe shekaru uku ko fiye da haka, daga nan kuma zai wuce jami’a yana ɗan 18.”

Daga ƙarshe ministan ya ce “daga yanzu hukumomin NECO da WAEC ba za su ƙyale duk yaron da bai kai 18 ya zauna jarrabawar kammala sakandare ba…”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *