Kakakin Rundunar yansadan Kano ya ziyarci kwamishinan yada labarai

Spread the love

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ziyarci kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, domin samar da alakar inganta tsaro a jihar.

Lokacin da yake jawabi SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun ziyarci kwamishinan ne domin taya shi murnar mukamin da gwamnan Kano ya ba shi, sannan su kyautata alakar aiki tsakanin yan sanda da ma’aikatar yada labarai ta Kano.

Kiyawa ya jaddada cewa akwai bukatar rundunarsu ta hada kai da ma’aikatar don kyautata harkokin yada labarai da kuma shigo da mutanen Kano kan harkokin tsaron jihar.

Da yake nasa jawabin kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya yaba da ziyarar kuma ya nada tabbacin ziyarar zata kara inganta alakar ma’aikatar da Rundunar yan sadan, domin samar da ingantattun bayanai don kyautata tsaron jihar.

Ya ba da tabbacin ma’aikatar zata cigaba da aiki kafada da kafada da rundunar yan sandan don wayar da kan al’umma su fahimci muhimmancin taimakawa yan sanda don inganta tsaron jihar Kano.

Waiya ya ce Wannan kyakykyawar alakar zata taimaka wajen kara samar da fahimtar juna tsakanin yan sanda da jama’a da don samun sahihan labaran da za su kara tabbatar da tsaro a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *