Kallo ya koma sama: Kakakin kotun Musulinci a Kano Muzammil A. Fagge ya bayyana cewa ma su gabatar da kara ne suka ari Murja Kunya don tuntubarta kan wani zargi.

Spread the love
Murja Kunya

Sakin Murja Ibrahim Kunya, ya ya mutsa hazo a shafukan sada zumunta, da kuma jahar Kano wadda ake kallon ta, a matsayin madubi wajen aiwatar da dokoki na shari’ar addinin musulinci.

Sai dai yin amfani da shafukan sada zumuntar da wasu matasa ke yi ta hanyoyin da ba su dace ba, na kara lalata tarbiyar yara da koyon munanan dabi’u ciki harda kananan yara.

Idan ba a manta ba, jaridar Idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewa, hukumar hisbah ta jahar Kano, ta kama yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya, bayan al’ummar Unguwar Tishama sun yi korafin ta, bisa zargin ta da aikata laifukan da suka ci karo da koyarwar addinin musulinci.

Hukumar Hisbar bisa jagorancin babban kwamandan ta, Asheik Mallam Aminu Ibrahim Daurawa, su ne suka jagoranci gurfanar da ita a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP, bisa zargin , aikata badala, kawo batagari cikin dare, tada hatsaniya da kuma tsoratarwa.

Bayan karanto mata kunshin tuhumar da ake yi mata nan ta ke ta musanta, kuma lauyan dake kare ta ya roki kotun ta sanya ta a hannun beli.

Sai dai mai gabatar da kara bai yi suka ba kan rokan bayar da belin na ta.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya aike da ita zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya , har zuwa ranar 20/2/2024 domin yin nazari kan bayar da belin ta ko akasin haka.

Kwanaki biyu da yin shari’ar ne rahotanni suka bayyana cewa, Murja Ibrahim Kunya , ta fita daga gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya , inda labarin ya karade Duniya musamman ma jahar Kano, da ake kallo jahar dake hani da aikata mummuna.

To sai dai mai Magana da yawun hukumar gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya na Jihar Kano Musbahu Lawan, ya shaida cewa, kotu ce ta Aike da Murja Kunya zuwa Gidan Gyaran Hali, kuma ita ce ta bayar da umarnin a sake ta.

Ya Kara da cewa basa bayar da duk wanda suke tsare da shi, sai da umarnin Kotu, kuma haka aka yi.

Wata majiya daga hukumar hisbah ta jahar Kano, ta bayyana cewa suma labari suka ji, a gari na sakin Murja Kunya.

Hukumar Hisbah ta kama Wasu Yara da ke Roƙo da Barace-Barace a Kano

Legas za ta hana amfani da robar tekawe daga gobe Litinin

A Talatar da ta gabata dai Mukaddashiyar babban kwamandan hisbah bangaren mata Dr. Khadija Sagir Sulaiman, ta bayyana cewa , gwamnan Kano ya ba su umarnin yin aikin ba tare da wani ya yi mu su katsalandan ba.

Harma Dr. Khadijan ta musanta zargin da ake yi kan Murja Kunya, na kin kama tunda wuri sakamakon ta na goyon bayan gwamantin jahar Kano.

” Ba haka ba ne , duk wanda aka samu da aikata rashin da a doka zata yi aiki akansa , kuma zu ci gaba da kama yan Tiktok dake wallafa fitsara”.

A na su bangaren Kakakin Manyan kotunan shari’ar addinin musulinci na jahar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa rade-radin da ake ta yi cewar Murja Kunya, an sake ta ko an bada ita beli , magana ta gaskiya Murja, ta na waje tun ranar Alhamis.

Mizammil Ado Fagge ya ce sun tuntuni kotun da ake yin shari’ar , inda ta shaida mu su cewar, Lauyoyin ma su gabatar da kara ne , suka zo suka ari Murja , domin ci gaba da tuntubarta kan wani zargi dake kara bibiyarta.

” Amma ba abun mamaki ba ne dan an bayar da belin Murja Kunya, saboda na farko wannan laifi da ta yi ba laifi ba ne wanda za a ki bayar da ita beli” Muzammil Fagge”.

Ya kara da cewa, Hurimin kotu ne na ta bada beli ko ta hana , amma dai magana ta gaskiya Murja ba ta gidan gyaran hali tun ranar Alhamis.

” wannan ba sabon abu ne, sai dai kawai ita saboda labarin ya ya mutsa hazo kuma ga abubuwan da ta ke yi , wanda ya saba da al’ada da kuma addinin mu na Musulinci shi yasa mutane kowa hankalina ya tafi akai”.

A lokacin gwamnatin tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, aka fara gurfanar da ita, bisa yada kalaman batsa da rashin tarbiya, har a wancan lokacin aka yanke mata hukuncin yin shara , a Asibitin Murtala Muhammed dake kwaryar birnin Kano.

Sai dai al’umma na ganin aiyukan rashin da’ar da Murja Kunya ke yi, kara yawa suke yi, shi yasa ma hukumar hisbar ta kamo ta, don tauna aya dan tsakuwa taji tsoro.

Yanzu kallo ya koma sama ga kotun shari’ar addinin musulincin kan hukuncin da zata yanke wa Murja Kunya, idan ta same ta da laifi, da kuma kalubalen da ke gaban hukumar hisbar bisa , zargin tsoma bakin wasu yan siyasa kan sakin Murja Kunya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *