Kallo Ya Koma Sama: Yadda Aka Gudanar Da Shagalin Bikin Aure Mai Cike Da Abun Mamaki A Kano.

Spread the love

Daga Dauda Muhammed Baban Ameera.

Wasu ma’aurata sun tsayar da komai cak yayin da suka bayyana cikin wata shiga ba Kamar yadda aka saba ganin Amarya da Ango a wannan zamani ba.

Kamar yadda ake gani a cikin wannan  hoto na amaryar da matashin  ya Aura ta fito, wajen  shagalin bikin  sanye da Hijjabi, Nikab da safar hannu da ta  Kafa inda ta rufe dukkanin ilahirin jikinta a lokacin da ake tsaka da gudanar da murnar bikinta.

A yayin da Amarya ta fito cikin wannan shiga nan ta ke mai kula da kayan sauti DJ ya yi hanzari ya kunna wani take irin na kasar Larabawa wanda ya yi daidai da irin wannan shiga ta kasaita ta Amarya.

Wannan lamari dai wajibi ne ya zo wa wasu daga cikin al’umma da mamaki sakamakon yadda ake ganin wasu Amare a yayin gudanar da shagalin bukinsu, suke sanya kaya mai bayyana surar jiki wai da sunan murna amma sam hakan ba abu ne mai kyau ba.

Ko zaku iya daukar irin wannan salo a lokacin bukukuwan ku??? Muna jiran sakonninku, ta wannan link Na facebook. na idongari https://www.facebook.com/share/p/NUPbvA8MiFnDUfp7/?mibextid=qi2Omg

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *