Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Alaska Airlines ya dakatar da aiki da jiragensa ƙirar Boeing 737 Max 9 bayan tagar ɗaya daga cikinsu ta ɓalle hanhai ana tsaka da tafiya a sama.
Sai dai dukkan fasinjoji saba’in da bakwai da kuma ma’aikata sun sauka lami lafiya a Portland ‘yan mintuna bayan faruwar lamarin a ranar Juma’a da yamma.
Jirgin samfurin 737 Max na da tarihin matsaloli, inda a 2019 ma aka jingine shi a duniya baki ɗaya bayan haɗurran ya yi a Indoneisa da Habasha.