Kamfanin mai na Dangote ya bayyana yi wa ‘yan kasuwa da ke saro man fetur a matatarsa ragin kuɗin man.
Cikin wata sanarwa da babban jami’in sadarwar kamfanin, Anthony Chiejina ya fitar ranar Lahadi ta ce an rage wa ‘yan kasuwar farashin da suke saro man daga naira 990 zuwa naira 970, domin ”nuna godiyarsa ga ‘yan Najeriya”.
”A yayin da shekarar nan ke zuwa ƙarshe, wannan ita ce hanyar da za mu gode wa mutanen Najeriya kan irin goyon bayan da suka riƙa nuna mana har matatarmu ta tabbata. Wannan ƙari ne kan godiyar da muke yi wa gwamnati bisa goyon bayan da ta ba mu wajen ɗaukar matakan da suƙa ƙarfafa wa kamfanonin cikin gida gwiwa”.
Sanarwar ta ƙara da cewa matatar ba za ta yi wani abu da zai rage ingancin man da take tacewa ba, wanda ta ce ingantacce ne da ba ya gurɓata muhalli.
Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki da matatar ta fara fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje somin sayarwa