Kamfanin Meta ya ce zai toshe kafofin yaɗa labaran Rasha

Spread the love

Kamfanin Meta ya ce zai toshe kafofin yada labaran kasar Rasha daga shafukansa na sada zumunta saboda suna amfani da su wajen yada farfagandarsu.

Kamfanin da ya mallaki shafin Facebook ya ce zai fadada takunkumi da ya sanyawa kafofin na Rasha da suka hada da tashar RT da Rossiya Segodnya.

Nan da ‘yan kwanaki kadan haramci zai soma aiki. Meta yace a baya an bata samunsu da irin wannan da’a kuma ko a yanzu abubuwa basu sauya ba.

Tashar RT ta yi alla-wadai da matakin tana mai cewa tauye yancin aikin ‘yan jarida ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *