Kankarar da ake sayarwa kan kudi Naira 100 guda daya kafin zuwan watan azumi, yanzu duk guda daya ta koma Naira 700 a cikin birnin Kano.
Majiyar jaridar idongari.ng wato jaridar indaranka, wadda ta yi bincike kan dalilin da ya haddasa tsadar kankarar da kuma ko masu sayarwar suna samun ribar da ya kamata saboda kukan da suka yi na cewa karancin wutar lantarki ya taimaka wajen tashin farashin nata.
Suleiman da ke saro kankarar ya kuma sayar, ya ce suna amfani da watan azumi ne suna sayo kankarar suna sayarwar suna dan samun abin da ya samu, don su samu abin da ba a rasa ba.
“Ba wuta a yanzu, inda muke saro kankarar dole su kara kudi, saboda da inji suke amfani su ma, shi yasa mu ma muke kara kudi don mu mayar da uwar kudin, sannan mu samu na rufawa kai asiri,” in ji ta
Suleiman, ya ce suna saro manyan kankarar a kan Naira 500 su yi kudin mota sannan kuma su sayar a kan Naira 700, amma a hakan wata takan zama asara domin ta kan tsiyaye kafin su sayar, a karshe suna iya samun ribar Naira 100 ko 150 a kan kowacce kankara.
Ya ce hakan yana taimaka musu, ya fi su zauna ba sa yn komai, kuma ba don karancin wutar lantarki da kuma tsadar da ta yi ba, da za su iya samun riba fiye da yadda suke samu a yanzu.
Wata mai gidan sayar da kankarar a unguwar Dakata , Mubarak ,ya ce yana sana’ar sayar da kankara shekara Uku, amma ba su taba fuskantar tsadar ruwa da wutar lantarki irin na wannan lokacin ba.
Ya kuma ce ruwa ma da suke saya a tankuna ya kara kudi, ledar kulla ruwan ta yi tsada, bare uwa-uba wutar lantarki ta yi karanci ga kuma tsada, shi kuma janareto ba zai musu abin da suke so ba.
Wani magidanci mai sayan kankara yau da kullum, Musa Naseer ya ce a kullum yana sayan kankarar Naira 1,000 ko 700 a gidansa wanda a baya ba ta wuce ta Naira 100 zuwa 150 da ya ke saya ba.
“Wato gaskiya ana cikin wani hali, a bara kankarar dana ke saya ba ta wuce ta 600 baki daya, amma yanzu tana haura 1,000 ma,” a cewarsa.