Kano: Abba ya miƙa buƙatar neman ƙarin kasafin N99bn

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nemi Majalisar Dokokin Jihar ta amince masa da ƙarin kasafin kuɗi na naira 99,221,503,569.90 domin cike giɓin kasafin shekarar 2024.

An gabatar da buƙatar gwamnan ce a zaman majalisar, wanda aka yi a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Ismail Falgore, wanda ya bayyana cewa an buƙaci ƙarin ne bisa dogaro da sashi 122 (A) da (B) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin sauƙaƙa wa gwamnatin wajen yin wasu ayyukan more rayuwa domin al’ummar Jihar Kano.

MB Talla

Bayan gabatar da kasafin, Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Musa Shanono ya bayyana wa manema labarai cewa ainihin Kasafin 2024 na jihar, Naira 437,338,312,787, idan aka amince da ƙarin kasafin, jimillar kasafin na 2024 zai koma 536,559,816,357.84.

Shanono ya yi bayanin cewa za a yi amfani da ƙarin kasafin wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi, da sauran abubuwa.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin ta ƙuduri aniyar cigaba da aiwatar da wasu muhimman ayyuka da kuma inganta rayuwar mutanen jihar, musamman a ɓangaren kiwon lafiya da ilimi.

Bayan haka kuma, a zaman, Yusuf Aliyu, mamba mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ya buƙaci gwamnatin ta gyara tare da sake gina filin wasa na Gwagwarawa.

Aliyu ya ce filin wasan ya zama matattara mashaya miyagun ƙwayoyi, wanda hakan ke barazana da tsaro a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *