Kano: An Fara Binciken Matashin Da Ake Zargi Da Fisgo Hoton Alkalin Alkalai A Kotu Sannan Ya Buga A Kasa.

Spread the love

Ana zargin Wani matashi Mai suna, D. Shehu Ado, mazaunin unguwar Sagagi, ya shiga kotun shari’ar addinin musulinci ta CT Number 1, dake Kofar kudu Kano, Inda ya dauko hoton alkalin alkalai na jahar,Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, dake Saman wajen zaman alkali ya buga a  kasa.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa , nan ta ke mutane suka rike,  Wanda Ake Zargin tare da danka shi a Hannun jami’an Yan Sandan Kano.

Lamarin dai ya Faru ne bayan da alkalin kotun ya kammala sauraren Shari’a a ranar Laraba.

Wanda Ake Zargin ya shaida cewa ya gaji da Duniya sakamakon yau Kwana Uku Bai samu ya ci abinci ba , shi yasa ya aikata hakan don a yanke masa hukuncin kisa.

Kakakin manyan kotunan Shari’ar addinin musulinci na jahar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa, yanzu za su Jira domin ganin chajin da Yan Sanda za su Yi masa.

Muzammil Ado, ya kara da cewa, duk da suna jiran sakamakon binciken Yan Sandan, amma Wanda Ake Zargin ya aikata laifuka da suka hada da, Yunkurin kashe Kansa, Barna ta hanyar Buga hoto da kasa.

” Laifin Yunkurin kashe Kai hukuncinsa ya Kai shekaru Uku sai laifin barna shi kuma shakara Daya” Muzammil Ado Fagge “.

Haka zalika ana zargin matashin da yin zage-zage a kotun da kuma tayar da hankali, kuma bayan kammala bincike Yan Sanda za su Gurfanar da shi a gaban Kotu Mai hurumi.

Kakakin kotunan Shari’ar addinin musulincin, ya ce rayuce wadda ta zama dole , sai kana Yi jama’a uziri duba da yanayin da ake ciki, Amma wasu suna sane suke aikata laifuka , Inda ya ce ba za su yadda da haan ba, domin Kotu ba wajen wasa ba ne.

” Ba zai yiwu ba Wani ya zo ya tsallake kowa da kowa ya dauko hoton alkalin alkalai, kuma ya dinga kokarin zai kashe Kansa, amma ya dinga cewa kwanansa biyu zuwa Uku Bai ci abinci ba” Muzammil Ado “.

Ya kara da cewa Wanda Ake Zargin lafiyayyen mutum ne , Mai lafiya a jiki, Mai karfi har ya Yi tsalle ya chakumo hoton dake rataye a sama tare da ikirarin kashe Kansa bayan ya buga Hoton da kasa.

Wanda Ake ya shaida wa , Idongari.ng, cewa matsin rayuwar ce, ta Sanya shi aikata hakan don a yanke masa hukuncin kisa.

Yanzu haka dai jami’an Yan Sandan jahar Kano. Sun tafi da shi zuwa babban sashin gudanar da binciken laifuka na CID, don fadada bincike akansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *