Kano: An Kara Yawan Jami’an Tsaro A Kasuwar Hatsi Ta Dawanau Saboda Yunkurin Wawushe Kaya.

Spread the love

Bata-gari sun yi yunkurin kutsawa su sace kayayyakin abinci a Kasuwar Hatsi ta Kasa da kasa da ke Dawanau a Jihar Kano da sunan zanga-zangar tsadar rayuwa

Hukumar gudanarwar kasuwar ta ce a sakamakon haka tadauki karin jami’an tsaro sama da 800 domin tabbatar da tsaron kasuwar.

Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Dawanau, Alhaji Muntaka Isa, ya ce hadin gwiwar da suka samu daga sojojin da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaron jihar, ya kara inganta tsaro a kasuwar.

Shugaban kungiyar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin cewa matakin zai kare kasuwar yadda ya kamata daga barna da sata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *