Daurawan matasa a garin jama’ar Kwagwar dake Karamar Hukumar Gezawa sun rufe babban Masallacin garin tare da hana Sabon Limamin Garin Jan Sallar Juma’a saboda zargin rashin cancantarsa .
A makon da ya gabata ne Alumar garin na Jama’ar Kwagwar suka zargi Dagacinsu da Hakimin Gezawa da Masarautar Gaya da Kuma Baturen Yan Sanda na Gezawa DPO da kakaba wa Al’ummar garin sabon limamin da basa so saboda zargin rashin cancantarsa wato Malam Ibrahim Audu.
Dattawa da matasan garin sunyi zargin amfani da Kudi wajen nadin sabon limamamin daga Dagacin Garin zuwa fadar Hakimin Gezawa har zuwa fadar Masarautar Gaya .
- Lassa ta kashe mutum 150 cikin jihohi 24 a Najeriya – NCDC
- Sojojin Nigeria Sun Yi Fata-Fata Da Sansanonin Yan Ta’adda Guda Uku A Zamfara
Bayan mutuwar tsohon Limamamin Malam Aminu Ma’aruf sai Hakimin Gezawa ya nada Dansa Malam Tajudden Aminu Amma daga baya Hakimin ya warware nadin nasa aka nada wani daban saboda zargin bada cin hanci .
Tuni dai matasan garin na Jama’ar Kwagwar suka sake shirya zanga zanga tare da rufe duk wata hanya ta shiga Masallacin wanda haka yasa ba,ayi sallar Juma’a a Masallacin ba a Karon farko.
Haka kowa ya hakura ya koma gida ciki harda sabon limamamin wasu kuma sukaje masallaci mafi kusa dasu.
RAHMA RADIO