Kano: INEC ta dakatar da zaben karamar hukumar Kunchi, bayan yan daba sun gudu da kayan zabe

Spread the love

Hukumar zabe mai zaman kanta, ta kasa reshen jahar Kano, ta dakatar da zaben karamar hukumar Kunchi, biyo bayan yadda wasu yan daba suka tarwatsa kayan zaben da yunkurin farwa jami’an INEC.

Kwamishinan zaben jahar Kano, Ambasado Abdu Zango, ya bayyana cewa, yan dabar sun kwashe kayan zaben, inda sukaje da gamayyar hukumomin tsaro , suka taho da ma’aikatan zaben domin tseratar da lafiyarsu.

Ya kara da cewa sauran kananan hukumomi biyar da suka hada da , Tsanyawa, Rimin Gado, Tofa, Kura, Garin Mallam, an gudanar da zaben in banda kunchi da aka dakatar da zaben.

Kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa yanzu haka jami’an tsaro sunanan a yankin domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kuma kare rayukan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *