Kano: Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda

Spread the love

Kotun majistire mai 32, dake zaman ta a unguwar Norman’Sland Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Abdul’aziz Habib, ta bayar da belin dan siyasar nan Danbilki Kwamanda.

Tunda fari ana zargin Danbilki Kwamanda, da laifin furta wasu kalamai da za su iya haifar da rudani ga al’umma, musamman kan abunda ya shafi masarautun jahar Kano guda 5.

Mai gabatar da kara Barista Bashir Saleh ya shaida wa kotun cewa hakan ya saba da sashe na 114 a Kundin Sharia Penel code.

Sai dai wanda ake karar ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa, dalilin da lauyansa, Barista Ibrahim Chedi ya nemi kotun ta bayar da belinsa.

Sharudan Belin da kotun ta gidanya wa, wanda ake zargin sun hada da mutane biyu da za su tsaya masa, wajibi ne kuma daya ya zama babban sakataren gwamnatin jahar Kano da kuma Hakimi.

EFCC na bincike kan yarjejeniyar Nigeria Air – Keyamo

Yadda gobara ta ƙone wani coci ƙurmus a Legas

Haka zalika  su a ajiye kudi naira miliyan daya da hotunan su harda na wanda ake zargin.

Mai shari’a Abdul’aziz Habib ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Fabarairun 2024 , don ci gaba da sauraren shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *