Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Ci Gaban Shari’ar Da Aka Yi Karar KANSIEC Da Mutane 3 Kan Kudin Siyan Form Miliyan 10 Ga Yan Takarar shugaban karamar hukumar.

Spread the love

 

Wata Babar kotun jahar Kano dake zaman ta, a unguwar Miller Road, ta sanya ranar 22 ga watan Oktoba 2024 don ci gaba da sauraren Shari’ar dake Tsakanin Umar Ibrahim Umar da kuma hukumar Zaben Kano.

Umar Ibrahim Umar, ya Garzaya gaban kotun ne domin kalubalantar hukumar Zaben Kano wato KANSIEC, kan Sanya naira Miliyan 10 ga mai neman takarar shugaban karamar hukumar sai kumi Miliyan 5 a matsayin na Dan takarar Kansila a shirye-shiryen da hukumar ke Yi na gudanar da Zaben a ranar 26 ga watan Oktoba 2024.

A kunshin takaddar karar Mai namba K/642/2024, ana karar, Hukumar Zaben Kano (KANSIEC) , majalissar dokokin Kano, Gwamnan Kano da kuma kwamishinan shari’a na jahar Kano.

Wanda ya Yi karar ya shaida wa, IDONGARI.NG, cewa duba da yanayin da ake ciki kudin da hukumar ta Sanya sun Yi yawa, kuma yin hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Nigeria sashi na 7 (4) cikin baka da sashi na 126 da kuma 107 domin barazana ce ga Demokuradiya.

” domin a fahimta ta Demokuradiya ba a yin ta da kudi, to kuma wannan Miliyan 10 da aka saka zai zanyo ta ke hakkokin matasa da dama da wadanda suka cancanci su shugabanci al’umma Amma ba su da dama” cewar Umar I Umar “.

Ya kara da cewa kasancewar a wannan kadami da Ake ciki don ganin an tabbatar da shugabanci nagari, tabbas Sanya kudi a Wani tsari na yin takara mafarkin yaki da cin hanci da rashawa ba zai cika ba.

” Abunda ya sa muke karar majalissar dokokin jahar Kano, ita ce ta Yi dokar har hukumar Zaben ta Yi amfani da shi ta Sanya Miliyan 10 duk da cewar domar ba ta faiyace adadin kudin da za a saka ba.

Haka zalika ya Yi karar Gwamnan Kano, bisa dalilinsa na Sanya Hannu kan dokar, domin da ace Bai Sanya Hannu ba , ba zata zama doka ba, Kuma dokar ta ci karo da kundin tsarin mulkin Nigeria.

Na hudunsu shi ne kwamishinan Shari’a na jahar Kano, bisa Zargin da suke Yi masa na rashin yin aikinsa na ba wa Gwamnan jahar Shawara kan abinda ya shafi dokoki.

Don haka ne muka tafi babbar kotun jaha, ta Yi mana fassarar sashi na 51 hukumar Zaben Kano KANSIEC, ta dogara da shi har ta Sanya kudin da Wuce hankali.

Tunda fari AlÆ™aliyar alkalan Kano , Justice Dije Audu Aboki, ce ta fara sauraren Shari’ar, a ranar 14 ga watan Oktoba 2024, Inda ta mayar da Shari’ar zuwa wata babbar kotun jaha Kano, karkashin jagorancin Justice Maiwada don ci gaba da sauraren Shari’ar, a ranar 22 ga watan Oktoba 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *