Babbar kotun tarayya mai lamba 2 dake zaman ta a jahar Kano, karkashin jagorancin Justice M.N.Yunusa, ta yanke hukuncin daurin watanni shida-shida a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya, ga wasu mutane 17, da aka samu da aikata laifin siyar da kudaden ketare ba tare da samun Lasisi ba.
Mai gabatar da Kara, ya karanto wa dukkan mutane 17 kunshin tuhumar da ake yi mu su , wadanda Suka amsa laifin.
Idan ba a manta ba , jaridar idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewar , rundunar Yan Sandan jahar Kano tare da hadin gwiwar jami’an hukumar tsaron farin kaya DSS, ne Suka Kai wani sumame a Kasuwar Yan chanji ta Wappa dake jahar , inda Suka kamo wadanda ake zargin sannan Suka Gurfanar da su a gaban kotu.
Wadanda kotun ta yanke wa hukunci, sun hada da , Ayuba Ibrahim, Idris Sa’idu, Idris Usman , Sha’aibu Muhammad, Hamisu Iliyasu ,l, Usman Hassan, Kamal Aminu, Muhammad Yunusa da Buhari Junaidu.
Sauran sun sune Isma’il Salisu, Rabi’u Muhammad Magashi, Muhmud Sani , Halifa Ahmed Tijjani, Abdulmumuni Sani , Adamu Nuhu, Isah Abdulmumin da kuma Abubakar Kalla Musa.
Laifin ya ci Karo da sashi da sashi 57 (5) (b) na dokokin bankuna da hada-hadar kudi na shekarar 2020.
Mai shari’a M.N. Yunusa, ya yanke mu su hukuncin daurin watanni shida-shida, a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya ko zabin biyan tarar naira dubu hamsin-hamsin kowanne su (50,000).
- Yan Sanda Sun Cafke Magidanci Bisa Zargin Shirya Taron Gangi Da Ya Janyo Rikicin Fadan Daba A Kano.
- NLC Ta Rufe Ofishin NERC