Wata babbar kotun jahar Kano,karkashin jagorancin mai shari’a Justice Yusuf Ubale, ta dage ci gaba da sauraren shari’ar da ake yi wa matar nan da ake zargi da yin garkuwa da kuma halaka yar abokin mijinta ta hanyar jefa ta cikin Rijiya a unguwar Tukuntawa dake jahar.
A zaman kotun matar mai suna, Fadila Adamu, ta fara kare kanta bisa zargin da ake yi mata, inda ta yi bayani dalla-dalla.
Lauyar da ta ke kare ta Barista Zulaihat Tata, ta yi mata tambayoyi, ciki harda cewa ta san tuhumar da ake yi mata inda ta amsa da cewar tasani.
Sannan lauyar ta bukaci wadda ake zargin ta yi bayanin yadda aka samu rigar Yarta a jikin Yarinyar da ake zargin ta halaka ta hanyar jefa ta rijiya.
Wadda ake tuhumar ta bayyana wa kotun cewa, tasha duka ne a wajen jami’an tsaro lokacin da ake yi mata tambayoyi shi yasa ta amsa.
Ana zargin Fadila ta dauki yarinyar mai suna Aisha Sani, sannan ta yi garkuwa da ita kuma ta halaka ta, ta hanyar jefa ta a cikin rijiya.
Kotun ta dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba 2024.
- Hukumar NSCDC A Jigawa Ta Ce Jami’an Ta 1800 Ne Za Su Bayar Da tsaro A Zaben Kananan Hukumomi.
- Kotu ta haramta wa VIO kamawa da cin tarar masu ababen hawa