Kano: Matasa Sun Rasu A Yunkurin Kama Wanda Ake Zargi Da Tura Alert Na Bogi

Spread the love

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku, a cikin wani Kududdufi dake unguwar Gwazaye karamar hukumar Kumbotso kano.

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, sun karbi kiran neman agajin gaggawa daga wajen wani mai suna Garba Sani, inda ya sanar da su faruwar iftila’in fadawar mutanen a cikin kududdufi akan titin Ring Road kusa da Dorayi Babba, bayan samun labarin ne jami’ansu suka fita zuwa wurin, inda suka iske cewar wasu matasa ne biyu da suka hada da, Saifullahi Muhammad da kuma Halifa Abdullahi, dukkansu mazauna unguwar Gwammaja, wadanda suka biyo wani mutum mai shekaru 30 daga kasuwar Kofar ruwa, zuwa inda lamarin ya faru kuma da zuwansu ne sai yaga cewar sun yi yunkurin cimmansa, inda ya fafa ruwan su kuma suka bishi cikin kududdufin.

Rahotanni na cewa dukkan matasan uku sun kasa fitowa bayan fadarwarsu ruwan, har sai da jami’an hukumar suka fito da su kuma dukkansu basa cikin haiyacinsu , kuma an dauke zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano, don dubawar jami’an lafiya wanda daga baya aka samu tabbacin sun rasu.

Saminu Yusuf Abdullahi, ya kara da cewa jami’ansu sun mika su hannun jami’in dan sanda mai suna Insfekta Halifa Muhammad, wanda yake aiki a ofishin yan sanda na Kuntau Kano.

Wani dan uwan daya daga cikin matasan da suka rasu , ya bayyana cewa ana zargin maatshin da ya fara fada cikin kududdufin, da damfarar jama’a ta hanyar tura musu Alert na bogi bayan ya yi sayayyar kaya a wajensu, inda ya cuci mutane da dama , kuma an biyo shi ne don aka mashi bisa cutar da yake yiwa al’umma a cikin kasuwanni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *