Kano: Matashin Da Ake Zargi Da Kunna Wa Mutane Wuta Ya Amsa Laifuka 3 A Gaban Kotun Musulinci

Spread the love

An Gurfanar da matashinnan mai suna Shafi’u Abubakar, a gaban babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Unguwar Rijiyar Zaki Kano, bisa Zargin sa da aikata Barna, Sanya Wuta da kuma kisan Kai da ganganci.

Tun a Ranar 15 ga watan Mayu 2024, rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta Samu labarin cewar Wanda ake zargin ya cinna wa Mutane wuta , a lokacin da yin sallar Asuba.

Daga bisa ni aka garzaya da su , asitibin Murtala Muhammed Kano, inda Limamin masallacin Sani Sulaiman, da kuma Mutane 13 Suka rasu, bayan Kai su asibiti da yan sanda Suka yi.

Babban auyan Gwamnatin jahar Kano kuma Kwamishinan Shari’a na jahar Barista Haruna Isah Dederi, ya jagoranci gabatar da karar tare da taimakawar Barista M. Salisu Tahir, Umar Yakubu, Bello Isah Lawan da Barista Ibrahim Arif Garba , a matsayin ma su Kara.

Kotun ta tambayi Wanda ake zargin KO shin Yana da lauyan dake kare shi, nan ta ke ya bayyana Mata cewar ba shi da lauya.

Sai dai kotun ta yi umarni a karanto masa kunshin tuhume-tuhume guda uku, da ake zarginsa da aikata wa, wadanda Suka hada da Barna ta Hanyar sanya wuta, sanadin mummunan rauni da kuma laifin kisan Kai , Wanda duka ya amsa laifukan uku , ba tare da ya wahalar da kansa ba.

Tuni dai kotun ta bayar da umarni ga hukumar da take bayar da gudunmawa ga mai karamin karfi , don su Samar masa da lauyan da zai kare shi a shari’ar.

Lauyoyin gwamnatin jahar Kano, sun bayyana cewa sun shirya gabatar da shaidun su, kan laifukan da ake zargin sa da aikata wa.

Bayan fitowa daga kotun , , jaridar idongari.ng , ta tattauna da , Shafi’u Abubakar, Wanda ake zargi da aikata laifukan inda ya bayyana cewar, babu abunda zai ce , amma ya amsa iya abunda ya faru a gaban kotu.

Ya Kara da cewa yanzu haka Yana jiran irin hukuncin da kotu za ta yanke masa.

Sai Wanda ake zargin ya ce an chanja masa zance kan maganar Gado KO kuma auren dole,kuma baya yin shaye -shaye balle ya Samu tab in hankali.

Kawo yanzu mutane 17 cikin 24 da aka kwantar a asibiti Suka rasa rayukansu, kamar yadda rundunar Yan Sandan jahar Kano bakin mai magana da yawun ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar.

Mai Shari’a Malam Halhalatu Kuza’i Zakariya ya bayar da umarni ga jami’angidan ajiya da gyaran hali da tarbiya su wuce da shi, har zuwa Ranar 31 ga watan Mayu 2024, don ci gaban shari’ar.

Kano: Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Mutane 17 Hukunci Bisa Samun Su Da Laifin Siyar Da Kudaden Wajen Ba Tare Da Lasisi Ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *