Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen ɗan majalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari/Tsanyawa.
Jam’iyyar ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da wasu ’yan siyasa sun yi maguɗi.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Kwamared Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya shaida wa ’yan jarida cewa INEC ta “tauye wa jama’a haƙƙinsu” bayan ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Ya ce zaɓen ya kamata a gudanar da shi ne a rumfunan zaɓe 10 da kotun ɗaukaka ƙara ta soke.
NNPP ta ce INEC ta ƙwace sakamakon da aka gudanar a rumfunan 10, tare da yin amfani da tsohon sakamakon da kotu ta riga ta soki.
- Gungun Yan Daba Sun Tare Motocin Yan Sanda Da Yan Jarida A Kano
- Gungun Yan Daba Sun Tare Motocin Yan Sanda Da Yan Jarida A Kano
“A Ghari, jama’a sun yi zaɓe lafiya a rumfunan 10, amma saboda maguɗi da wasu ’yan siyasa da jami’an INEC suka shirya, sai aka bayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya yi nasara,” in ji jam’iyyar.
NNPP ta kuma zargi INEC da bayyana sakamakon a hedikwatarta ta Kano maimakon a cibiyar tattara sakamako na mazaɓar, abin da ta ce ya bayar da damar tafka maguɗi.
Jam’iyyar ta yi alƙawarin ci gaba da ƙalubalantar abin da ta kira rashin adalci da nuna son kai.
Ta kuma ce sakamakon da jami’an rumfunan zaɓe suka sanya hannu a kai shi ne ya kamata a tabbatar da shi.
Sai dai NNPP ta yaba da zaɓen cike gurbi da aka yi a Shanono/Bagwai inda ɗan takararta ya yi nasara.
Jam’iyyar ta bayyana zaɓen a matsayin mai inganci, ta kuma gode wa jami’an tsaro da kuma jama’a da suka fito ƙwansu da kwarkwata suka kaɗa ƙuri’a.
“Muna girmama jarumtar jama’armu da suka tsaya tare da mu, suka kuma zaɓi ’yan takarar NNPP a dukkanin zaɓukan da aka gudanar,” in ji shugaban jam’iyyar.
INEC da APC ba su ce komai ba tukuna.