Kano: Rikicin Hanyar Ruwa Tsakanin Makota Da Jami’an DSS Ya Haifar Da Rudani.

Spread the love

 

Wasu mazauna unguwar Badawa Bus stop Kano, sun Zargi Wani babban jami’in hukumar tsaron Farin kaya DSS, da uzzurawa rayuwarsu , bayan Wani sabani da ya ratsa a Tsakanin su kan matsalar Kwata.

Al’ummar yankin sun Zargi jami’in DSS din , Wanda yake makota da su, yana debo yaransa daga Ofis, don haka ne suke kira ga Mahukunta su shiga tsakanin su domin Yi wa tufkar hanci.

A makon da ya gabata ne da ake Zargin wasu jami’an DSS, din sun Yi wa gidan makotan kawanya, tare da yin harbe-harbe da Bindiga Wanda hakan ya Sanya razani da tsora ga mazauna unguwar.

Rahotanni na cewa mutane biyu ne harbin Bindigar ya shafa da suka hada da, farar hula da kuma wani jami’in DSS, kamar yadda al’ummar yankin suka tabbatar.

Wakilin mai unguwar Badawa Musbahu Kasim , ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce Bai Yi tunanin hakan zai kasance ba , Amma yanzu haka bangarorin da lamarin ya shafa suna tattaunawa don warware matsalar.

Jami’an DSS din sun sako magidancin da suka kama , kan sabanin da aka samu kan hanyar ruwa da ake Zargin an toshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *