Kano ta sanar da sabuwar ranar komawa makarantu a jihar

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2024, a matsayin sabuwar ranar da za a koma makaratun kwana na firamare da na sakandare na gwamnati da kuma masu zaman kansu na zangon farko na shekarar 2024/2025.

Hakazalika ɗalibai a makarantun je-ka-ka-dawo a fadin jihar za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.

Idan dai ba a manta ba, kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ne ya sanar a ranar Asabar 7 ga watan Satumba, ɗage ranar da za a koma makaranta.

A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar, gwamnatin jihar ta buƙaci iyaye da su yi la’akari da sabon ranar da za a koma makaranta domin tabbatar da cikakken bin doka da oda.

Sanarwar ta kuma shawarci ɗaliban da su guji shiga da abubuwan da ba a yarda da su ba a makarantunsu da kuma ya saɓawa doka, kamar irin su wuƙaƙe ko reza, kuma su tabbatar da bin doka.

Sanarwar ta jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na ganin kowane yaro ya samu ilimi mai inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *