Kano : Wakilin Dagaci Dogon Kawo Muka Cire Ba Dagaci Ba: Hakimin Doguwa

Spread the love

Hakimin Doguwa, Alhaji Aliyu Harazumi, ya bayyana cewa bai dakatar da Dagacin garin Dogon kawon ba, a karamar hukumar Doguwa ta jahar Kano, kamar yadda ake yada wa a kwankin baya.

Sai dai Hakimin ya ce amma ya dakatar da wakilin Dagacin garin saboda zarge-zargrn sayar da gonakin da ake takaddama akansu.

Amma Dagacin garin Dogon Kawo, Alhaji Kailani Yusuf, ya zargi hakimin , da kokarin amfani da jami’an tsaro domin cin zarafinsa.

Dagacin ya ce hakimin ya sa jami’an tsaro su kama shi ba tare da sanin laifin da ya aikata ba, duk kuwa da lauyansa da ya tura ga yansanda da kai korafi wurinsu domin sanin dalili.

Hakimin, ya tabbatar wa da Premier radio cewa, shi bai cire dagacin ba wakilin dagacin ya cire saboda zage-zagen sayar da  gonakin da ake takaddama akansu.

Idan za a iya tinawa dai, a cikin watan Oktoban da ya gabata wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa hakimin ya dakatar da dagacin garin na Dogon Kawo, Alhaji Kailani Yusuf kan zargin sa da yi wa Fulani karfa-karfar kwace gonakinsu tare da sayarwa.

Sai dai dagacin ya musanta duka tuhume-tuhumen tare da kalubalantar matakin ta hanyar shigar da korafinsa zuwa ga masarautar Kano.
Ya ce babu wata sanarwa kan dalilin da ya sa shi hada shi da jami’an tsaron kuma babu wata sanarwa kan laifin da aikata masa, saboda yake ganin masarautar Kano ya kamata su je kasancewarsu masu rike sarauta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *