Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Kurna Kano, umarci magatakardar kotun ya rubuta takadda zuwa asibitin kula da ma su larular tabin hankali na Dawanau, don bincikar lafiyar wata mata mai suna Hajara, sakamakon wasu kalamai da ta furta bayan an gurfanar da ita a gaban kotun.
An gurfanar da matar bisa zargin aikata sata, inda mai gabatar da kara ya karanto mata kunshin tuhumar, amma ta ce ba zata ce komai ba, sai dai akaita wajen sarki don ta yi bayani.
Haka zalika ta bayyana cewa tafi karfin sata.
Kotun ta tambayeta, ko ta na da tabin hankali, amma taki cewa komai, sannan kotun ta ce ta kalli sama ta gani Fankoki na wa ne? a cikin kotun , namma ta ce babu wanda ya isa ya sata kallon Fanka.
- Hukumar CISA Tace Ba Za A Iya Yin Katsalanda A Zaben Shugaban Kasar Amurika Ba
- Za a fara rijistar baƙi a jihar Kano
Akarshe matar ta ce sai an biya ta kudin magani naira dubu dari biyu, sannan ta ce an kwashe mata wasu kaya a cikin ta.
Bayan haka ne wani mutum, ya daga hannu inda kotun ta bashi damar yin magana , kuma mutumin ya shaida wa kotun cewa yar uwarsa ce, wadda ake karar kuma tana da tabin hankali.
Akalin kotun mai shari’a Shamsiddini Ado Abdullahi, ya umarci magatagardar kotun ya rubuta takadda zuwa asibitin Dawanau, don duba lafiyar ta, sannan kotun ta dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Disamba 2024.