Kano: Yan Kasuwar Kaji Sun Koka Da Karancin Ciniki.

Spread the love

Ya yinda al’ummar musulmin duniya ke shirin gudanar da bukukuwan karamar Sallah a ranar Laraba, wasu ma su gudanar da sana’ar Kaji a jahar Kano, sun koka da karancin cinikin kajin a wannan shekarar ta 2024, sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a fadin Nigeria.

Guda daga cikin ma su sana’ar, akan Titin zuwa gidan Zoo , Mallam Bashir Maikaza , ya bayyana jaridar Idongari. ng, cewa a bana suna siyar da Jajayen Kaji Leya suna siyarwa kan Naira dubu biyar da dari biyar (5500) inda a shekarar da ta gabata suke siyarwa naira dubu uku Dari biyar 3500.

Mai Kaza ya Kara da cewa suna siyar kaji nau’in Bulara, yar sati shida kan naira 5500, inda a bara suke siyarwa naira 3500.

Ya kuma ce a shekarar bara anfi siyan kajin, fiye da wannan shekarar sakamakon matsin tattalin arzikin da al’ummar ke fuskanta.

Wani mai gyaran Kaji, Abba Zoo road, ya bayyana cewa shekarar da ta gabata , anfi cin kajin, domin an sun Gyara Kaji fiye da dubu daya.

Sai dai ya ce a wannan shekarar da wahala su Gyara Kaji guda 300, sakamakon matsanancin halin da ake ciki.

Abba ya Kara da cewa, kowacce kaza daya suna gyara ta akan naira 100 komai kankantar ta ko girmanta.

Bashir maikaza, ya shaida wa Wakilin mu , cewa karancin siyan kajin ne yake sanya su karya farashin su, duk da cewa sun siyo da tsada amma duk da haka suna yin asara.

Al’ummar dai na siyan kajin ne domin yin tuwon Sallah bayan kammala azumin watan Ramadana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *