Kano:Hukumar Hisba ta gurfanar da wasu mata bisa zarginsu da haifar da hatsaniya da Karuwanci a Sabuwar Gandu da Sabongari

Spread the love

 

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta gurfanar da wasu mata 4, a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta a unguwar Gama, karkashin jagorancin mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, bisa zarginsu da tayar da hatsiniya da harkar karuwanci a unguwar Sabuwar Gandu.

Matasan matan da aka gurfanar sun hada da, Saliha Usman, Hafsat Bashir, Fatima Adekunle da kuma Safiya Inusa.

Tunda fari mutanen Unguwar sabuwar Gandu , ne suka yi korafin, Saliha Usman da Hafsat Bashir , a hukumar hisba ta jahar Kano kamar yadda Idongari.ng, ya ruwaito.

Sai kuma Safiyya Inusa da Fatima Adekunle, aka kamo su a unguwar sabongari , lokacin da suke tsaka da aikata badala

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga..

An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba

Bayan gurganar da su a gaban kotun, mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su, karkashin sashi na 341, wadanda suka musanta zargin.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed , ya aike da su zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 15 ga watan Fabarairun 2024, dan ci gaba da shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *