Kano:Wata kotun musulinci ta yi umarnin tsare matasa 4 da ake zargi da yin Ludo, shaye-shaye a masallaci

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP Kano, ta aike da wasu matasa hudu zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya bisa zarginsu da hada kai wajen aikata laifi, cin zarafi tare da amfani da gwajin karfi.

Matasan da ake zargi sun hada da Sadik Ibrahim, Jamilu Ibrahim, Umar Ibrahim da kuma Adamu Ibrahim dukkan su yan uwan juna mazauna unguwar Rimin Kebe.

Tunda fari wani mai suna Auwalu Usman, mazaunin unguwar Rimin Kebe ne, ya yi korafi akan su , tare da cewa sun hada kai tare da shiga cikin masallaci suna yin Ludo da kuma shaye-shaye.

Mai korafin ya kara da cewa, bayan ya yi mu su magana, sai kawai suka taru har suka yi masa dukan tsiya tare da ikirarin cewar sai sun kaddamar masa , saboda ya yi mu su magana akan shaye-shayen da suke yi a masallaci dake unguwar Rimin Kebe.

Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su, inda wanda ake tuhuma na 1 ya amsa laifin sa, ya yin da na 2, 3, da na 4 suka musanta zargin.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya bada umarnin tsare su a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2024, domin gabatar da shaidu kan wadanda suka musanta zargin.

Yayin da mai gabatar da kara ya yi rokon kotun ta yanke wa, wanda ya amsa laifin sa hukunci a zaman kotun na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *