Karamin Ministan Man Fetur Da Iskar Gas Ya Yaba tare Jinjina A Wata Ziyarci Da Ya Kai Cibiyar Aikin Samar Da Wutar Lantarki Dake Maiduguri.
Karamin ministan albarkatun man fetur da Iskar Gas Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo ya yabawa kamfanin NNPC bisa nasarar aiwatar da manufofin shugaban kasa ta hanyar samar da ayyuka masu tasiri ga ‘yan kasa.
Wannan katafaren aiki guda ne cikin ire iren ayyuka samar da wutar lantarki ta gaggawa dake Maiduguri (MEPP) wanda Shugaban kasa Bola Tinubu ta kaddamar domin amfanar ‘yan kasa.
- Mun yi bankwana da ECOWAS babu batun dawowa – Nijar, Mali da Burkina Faso
- Kamaru Ta Zamo Kasar Farko Da Ta Fara Sayen Man Dangote Daga Ketare
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a cibiyar samar da lantarkin ranar Asabar, 14 ga watan Disamba, 2024.
Ministan wanda ya samu rakiyar shugaban rukunin kamfanin NNPC Ltd., Mele Kolo Kyari, da mataimakin shugaban kasa, da sauran masu ruwa da tsaki na kamfanin NNPC.
Ita dai cibiyar samar da lantarkin MEPP wani aikin hadakar wutar lantarki ne mai karfin megawatt 50 da aka kaddamar a ranar 2 ga Maris, 2023.
Rahotonni sunce tuni an riga an kammala aikin 32MW na aikin kuma tuni ya fara aiki, yayin da sauran Megawatt 18MW zai fara aiki cikin shekarar 2025 dake karatowa.