Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa masu zuba jari na ƙasar Qatar cewa su kai masa rahoton duk wani jami’in Najeriya da ya nemi a ba shi cin hanci.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen taron kasuwanci da zuba jari tsakanin ƴankasuwan Najeriyar da masu zuba jarin na Qatar, birnin Doha a ranar Lahadi.
Inda ya bayyana wa taron cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke neman kawo tsaiko ko kashe guiwar masu zuba jari a Najeriya.
“Na zo nan ne domin na baku tabbacin cewa muna yin garambawul. Duk wata matsala da wasunku suka fuskanta a baya, ya riga ya wuce, ba za ku gamu da irinta ba a nan gaba,” in ji Tinubu.
Inda ya ƙara da cewa “Kada ku bai wa kowa a cikin mutane na cin hanci, idan kuma har sun nema ko sun karɓa a hannunku, ku kawo ƙararsu wurina. za ku samu ganina.”
An karrama ɗan agajin da ya tsinci fiye da naira miliyan 100 ya mayar
Wasu Yan Daudu Sun Yi Wa Ofishin Hisbah Rotse Tare Da Kwantar Da Tutocinsu A Unguwar Bachirawa Kano.
Tinubu ya kuma bayyana musu cewa kuɗadensu za su kasance cikin aminci, yana mai cewa gwamnatinsa ta ƙarfafa batun yaƙi da cin hanci da rashawa da yaƙi da rashin tsaro.
Ministan masana’antu da kasuwanci na Qatar, Sheikh Mohammed bin Hamad bin Qassim Al Abdullah Al Thani, ya bayyana cewa ƙasarsa na sa ran yin amfani da damar da Najeriyar ta bayar, inda Qatar ɗin za ta fi bai fifiko sun haɗa da zuba sabbin jari a shirye-shiryen da suka shafi rage iska mai gurɓata muhalli da ma’adanai, sinadaran da ake samu daga ɗanyen mai, fannin masana’antu da kuma abubuwan ci.