Karon Farko Kwamishiniyar Mata Da Kananan Yara Ta Tallafa Wa Mata 200 Masu Larurar Yoyon Fitsarin A Kano

Spread the love

Kwamishinar ma’aikatar mata kananan yara da ma su bukata ta musamman ta jihar kano, Hajiya Aisha Lawan Saji rano, ta bayar da tallafin jari na Naira Dubu 30 ga kowacce mace don gudanar da sana’oin dogaro da kai, da inganta rayuwar su, ga mata masu larurar yoyon fitsari su 200 a jihar.

Kwamishiniyar ta bayar da tallafin ne a wani bangare na ci gaba da tunawa da ranar yaki da cin zarafin mata da kananan yara ta duniya.

Taron ya gudana ne a harabar inda aka ajiye masu larular yoyon fitsarin dake unguwar Kwalli,  inda Gidauniyar Fistula ta koyar da mata 200 sana’oin dogaro da kai domin samun damar taimakawa ‘yayan su da inganta rayuwar su musamman wadanda suke kula da su.

Kwamishinar ta yi kira ga mata da su dinga zuwa yin awo asibiti domin tabbatar da lafiyar su kafin Haihuwa domin gudun kamuwa da larurar yoyon fitsari.

Aisha Rano , tana daga cikin kwamishinonin da suka samu sauyin ma’aikatu a jihar kano, Wanda gwamnatin kano ta mayar da ita ma’aikatar kula da yawon Bude idanu da raya Al’adu ta jihar kano.

Wakilin mu ya zanta da Aisha Lawan Saji,  inda ta bayyana yanda shirin ya gudana tare da yin kira ga wadanda suka rabauta da tallafin domin yin amfani da shi ta hanyar da ta dace, harma da karfafa mu su gwiwa wajen zuwa asibiti domin tabbatar da koshin lafiyar su.

Shugabar dake kula da gidan masu yoyon fitsari ta jihar kano, Aisha Sani Kurawa, ta mika Godiya ga gwamnatin kano musamman ma’aikatar mata da kananan yara da masu bukata ta musamman a madadin mutanen da suka rabauta da tallafin kudin da za su ja jari, domin dogaro da kawunan su, tana mai cewar wannan shi ne karo na farko da aka taba ba wa masu larurar yoyon fitsari tallafi a jihar kano.

Ta kara cewar, a wannan karon ne suka taba ganin gwamnatin kano ta kula da wadannan mutane.

A nasu bangaren wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun nuna jin dadin su tare da alwashin yin amfani da tallafin kudin wajen yin sana’oin da suka koya.

Inda suka yaba wa kwamishiniyar bisa kokarin ta na ganin ta tuna da su a matsayin su na marasa lafiya.

Daga cikin mahalarta taron sun hadar da Daraktar kula da walwalar jama’a ta ma’aikatar mata, Hajiya Binta Yakasai, da Mataimakiyar shugabar jam’iyyar NNPP ta jihar kano, Hajiya Hauwa Fulani, da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *