Jama’a da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda ake kara samun matasan da suke hawa kan allon tallace-tallace musamman a arewacin Nijeriya, inda suke fatan hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin da ya dace don magance matsalar baki daya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wani matashi dan asalin jihar Katsina, ya hau saman Allon talla kusa da gadar Lado dake jihar Kano.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa matashin ya hau saman Allon tallan da misalin karfe 5:00am na asubashin ranar Laraba.
Hukumomin tsaro a jihar Kano tare da hadin gwiwar jama’a ne suka samu nasarar sauko dashi daga saman allon tallan.
Da farko dai matashin ya yi ikirarin cewa ba zai sauko ba har sai mawakinnan, Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya zo Sannan zai sauko daga saman.
Tun kafin sauko dashi, matashin ya fito da wani karfe da kuma sandunan da ya hau saman da su , inda yake kawo duka ga wadanda suka sauko dashi.
Mutane da dama sun yi fatan hukumomi za su dauki matakin magance wannan matsalar baki daya.
Wani mazaunin jihar Kano, ya bayyana cewa irin wannan dabi’a da wasu matasa suke yi bai kaama ba, domin akwai sana’o’in za su yi don dogaro da kansu amma irin wannan abu zubarwa da jihar Kano mutunci ne.
‘’ wannan ba tunani bane mai kyau ta yadda suke siyar da rayuwarsu’’.
Haka zalika wani ya kara da cewa sun zata masu sanya allon tallan ne, domin suna ganin lokacin da ya hau saman.
Daya daga cikin matasan da suka sauko dashi , Dan Amir Gyadi-gyadi, ya bayyana cewa lokacin da suka hau saman allon tallan sai da matashin ya zaro karfe yad inga kawo musu sara , amma basu ji tsoro ba kuma sun jure ne saboda dakile mummunar dabi’ar hawa saman da wasu matasa ke yi.
Ya kara da cewa bayan sun hau saman allon, ya shaida musu cewa ya tawo daga jihar Legos kuma yau kwanansa biyu bai ci abinci ba, shi yasa yace ba zai sauko ba har sai mawaki Dauda Kahutu Rarara ya zo.
‘’ a kwai wata jakarsa da aka sauko da ita hotunan Rarara ne a ciki da kuma lambar yabo da zai bashi’’.
‘’ munsha wahala kafin mu sauko dashi , domin ya buga mana karfe amma da kyar muka rike daga saman zuwa kasa.
Sai dai a karshe ya ce masu yin hakan wata kila talauci ne da ko kuma shiri don su yi suna musamman a shafukan sada zumunta.
- NCAA ta gayyaci kamfanonin jiragen saman cikin gida kan matsalar ɗage tashin jirage
- Gwamnatin Tinubu ta kusa fara cin bashi daga Opay – Dino
Koda a ranar 23 ga watan Yuni 2025 sai da rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto wani matashi mai suna Ibrahim Abubakar, mai shekaru 19 da ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar fadowa daga kan allon talla (billboard) akan gadar Ado Bayero kusa da kan titin zuwa Maiduguri Road a jihar.
Mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Hussaini Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aike wa da manema labarai bayan ceto matashin a waccan lokacin.
Rahotanni na cewa matashin yayi barazanar fadowa kasa matukar wani dan Tiktok mai suna Abdul BK bai zo ba.
DSP Hussaini, ya ce bayan samun rahotan kwamishinan yan sandan jihar , ya tura tawagar jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Kano, inda suka ziyarci wajen da gaggawa har aka ceto shi.
Sanarwar ta kara da cewa sakamakon, a wannin da matashin ya shafe a saman allon , ya wahala sosai saboda yunwar da yake ji, kuma bayan sauko dashi an garzaya dashi asibitin yan sanda dake unguwar Bompai don samun kulawar gaggawa.
Yanzu haka dai hukumomin tsaron yan sadan Kano da hukumar kashe gobara sun tafi ofishinsu don fadada bincike kan lamarin.