Kasa Ta Binne Akalla Mutane 50 A Wani Wurin Hakar Ma’adanai A Jihar Neja

Spread the love

Rahotanni daga kauyen farin Doki dake yankin Erana a karamar hukumar Shiroro na jihar Neja na nuna cewa, wani makeken rami da masu hakar zinari ke tona wa ya rufta da mutane akalla 50.

Tsohon Shugaban karamar hukumar Shiroro ASP Abdullahi Yarima Mai ritaya wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa ya ce bayan kwashe sa’o’i biyar da ruftawar ramin an samu zakulo mutane shida da ransu sai dai suna cikin wani mawuyacin hali.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja Abdullahi Baba Arah ya tabbatar wa Muryar Amurka da aukuwar lamarin, kuma ya ce jami’ansu na shirin zuwa wurin domin kai dauki, kuma suna cike da fatan samun wasu da dama, da kuma ransu.

Dama dai gwamnatin jihar Nejan ta haramta tona ma’adanan karkashin kasa ba akan ka’ida ba a jihar musamman a yankunan da kananan hukumomin ke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga.

VOA HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *