Kasar Senegal Na Shirin Fatattakar Sojojin Faransa.

Spread the love

Firaministan Senegal Ousmane Sonko, ya bayyana yiwuwar rufe sansanin sojin Farance da ke ƙasar.

Da yake jawabi a wajen wani taro a Dakar, ya ce me yasa har yanzu Senegal ke da sansanonin sojin Faransa shekaru 60 bayan samun ‘yancin kai daga Faransar.

Mista Sonko ya ce mene ne amfanin kasancewar sojin Faransa a ƙasar da ke da ‘yancin kanta?

Akwai sojojin Faransa kusan 350 a Senegal

Firaministan ya alƙawarta ƙarfafa dangantaka da Mali da Burkina Faso da kuma Nijar waɗanda tuni suka kori sojojin Faransa daga ƙasashensu sannan suka mayar da hankali wajen neman taimakon Rasha a yaƙin da suke da masu ikirarin jihadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *