Kashi 81 cikin ɗari na ma’aikatan Najeriya ba su da amfani’

Spread the love

Kusan kashi 81 cikin ɗari na ma’aikatan Najeriya ba sa wani ɓangare da ke samar da cigaba ga tattalin arziƙin ƙasar, in ji shugaban kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa na manufofi da tsare-tsaren kuɗi da sauye-sauye a haraji, Taiwo Oyedele.

Oyedele ya ce duk da cewa yawan marassa aiki a Najeriya kaɗan ne inda yake kashi 4.2 cikin ɗari, yawancin ‘yan ƙasar masu aiki ba su da wani amfani na ƙwarai ga tattalin arziƙin ƙasar.

Mista Oyedele ya ce Najeriya na mataki ɗaya ne da Birtaniya wajen yawan kashin marassa aikin yi wato 4.2 cikin ɗari, kuma abin da ya sa kenan har yanzu Najeriya ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi talauci a duniya.

An sanya dokar takaita zirga-zirga a kananan hukumomin Kano shida, da za a yi zaben ranar Asabar:

Ya ce akwai mutum sama da miliyan 113 da ke cikin fatara a Najeriya a shekara ta 2022, kuma yana ganin shakka babu yawan a yanzu ya fi haka domin a lokacin ba a janye tallafin mai ba da kuma daidaita farashin canjin dala.

Shugaban kwamitin na magana ne a wajen taron ƙoli na kasuwanci da zuba jari na Afirka a yau Alhamis, a Lagos.

Oyedele ya ce kasancewar Najeriya ba za ta iya sauya alƙibilar tattalin arziin duniya ba, amma yin sauye-sauye a manufofinta ka iya taimaka wa halin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *