Shugaban kasuwar kayan Gwari ta Yankaba dake jahar Kano, Alhaji Aminu Lawan nagawo, ya bayyana cewa yanzu duk wanda zai yi harkar kasuwanci a kasuwar sai sun san wakilinsa kafin su bashi damar fara kasuwanci.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa, daukar matakin ya biyo bayan zargin da ake yi wa, wasu matasa a cikin kasuwar da suka yi auren wasa da naira dari biyar Kacal ( N500).
Shugaban kasuwar ya kara da cewa, abun ya zo mu su da mamaki, idan aka yi la’akari da kasuwar wajen kare al’ummarsu da zamantakewarsu.
‘’ mu a matsayin mu na musulmi ba za mu dauki wannan da wasa ba’’.
- Ranar 8 ga Nuwamban 2025 za a yi zaɓen gwamnan Anambra – INEC
- Arzikin Ɗangote ya ninka zuwa dala biliyan 28 bayan fara aikin matatar mansa
Aminu Nagawo, ya ce matasan sun yi abun cikin jahilci, rashin tsari da kuma yarinta wadanda suka haddasa wannan lamari.
rahotanni na cewa an tura batun ga hukumar Hisbah ta jahar Kano, don daukar matakin da ya dace kan lamarin.
Sai dai saurayin da aka daurawa auren wasan ya gudu, bayan faruwar lamarin.
A ranar Talata da ta gaba ne, ake zargin saurayin da kuma budurwar wadda ta ke siyar da abinci a kasuwar Yankaban, suka shirya auren wasan da naira dari biyar kacal.
Nagawo, ya kara da cewa, wannan aure da suka yi , bai cika ka’ida ba, domin babu amincewar juna, Waliyan bangarorin biyu, Shaidu, Sadaki da kuma Siga don haka sun yi gaban kansu ne kawai.