Kaunar Murja Kunya ya ratsa cikin zuciya ta don haka ku Aura mun ita: Ustaz Assalafi

Spread the love

Daga B. Imam.

Wani Santalelen Ustaz Kuma matashi me jini a jika, ya roƙi Gwamnan kano, da Sarkin Kano dama kwamanda Hisba na Jihar Kano da su taimaka su Aura masa Fitacciyar ‘yar Tiktok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya da ta ke tsare a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiyya.

Matashin Ustaz din mai suna Ibrahim Assalafi dake zaune a unguwar Birget ya mika Ƙoƙon barar sa ga mahukunta  da su aura masa Murjahttps://ha.wikipedia.org/wiki/Murja_Ibrahim ,don ta zamo a matsayin matar sa kuma Uwar “ya”yan sa.

Assalafi ya ce, a halin yanzu babu wadda yake matuƙar Ƙauna irin Murja, duba da yadda son nata ya hana shi sukuni, Adan haka yake fatan ganin ya aure ta, ta yadda zai ceto ta daga ɗabi’u marasa kyau da take aikata wa.

Haka kuma mai fatan zama Angon Murja Kunya ya ƙara da cewar, Akwai wasu halaye da suka sanya ya ƙara son Murja ya ƙara Samun matsuguni a cikin zuciyar sa, waɗanda suka haɗar da fadar gaskiya da take yi komai ɗacin ta kuma ko kan waye, koda a kan kanta ne, dama yadda ba ta shiga abin da babu ruwan ta.

karan ta wannan labarinAna shirin mayar da wasu ofisoshin NUPRC daga Abuja zuwa Legas

karan ta wannan labarin Sojojin Najeriya sun sake gano wurin ƙera makamai a Plateau

Haka kuma ya ƙara da cewa a halin yanzu ya sadaukar da Rayuwar sa, domin yin jahadin Auren Murja Kunya ta yadda zai zama sanadiyyar shiriyar ta.

Baya ga haka kuma Assalafi ya ce yana da ƙwarin gwuiwar Murja Kunya za ta amince da shi da zarar ta ganshi, domin shi ɗin son kowa ne ƙin wadda ta rasa.

A karshe yaja hankalin mutane da su yi masa kyakykyawar fahimta tare da neman addu’ar fatan Alkhairi ta yadda zai zama Allah ya cika masa burin sa na samun nasarar Auran Jarumar Tiktok ɗin Murja Ibrahim Kunya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *