Al’ummar Baita, wani yanki da ke ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya sun yi kira ga gwamnati da ta taimaka wurin gina masu asibiti a yankin.
Mazauna wannan yankin na amfani ne da wani shago da ke da gado guda ɗaya kacal a cikinsa a matsayin asibiti sakamakon lalacewar asibitin da suke amfani da shi.
A cewar mazauna yankin ma’aikatan lafiya biyar ne ke kula da majinyata a asibitin.
A cewarsu sun samar da wurin ne a shekarar 1991 amma gwamnati ba ta kula da shi ba.
Mazauna yankin sun ƙara da cewa kusan mutane 10,000 ke ziyartar shagon a kowanne wata kuma mutane sukan zo daga ƙauyuka 10 da ke kewaye da kauyen na Baita.
Suna amfani da shagon ne kasancewar ba za su iya amfani da dan karamin asibiti na ainahi da ke kauyen ba sakamakon halin da yake ciki inda ginin ya tastsage.
Cikin shekara tara da suka gabata, sun yi ta yawo tsakanin shaguna da dama amma shekara biyu da suka wuce sun yi nasarar samun wani shago mai ɗaki biyu.
Yanzu, likita na amfani da ɗaki ɗaya wurin ganin marasa lafiya, yayin da ake amfani da daya ɗakin da ke da gado ɗaya kacal domin kwantar da majinyata.
Duk kuwa da wannan yanayi mazauna yankin ba su jin daɗin lamarin saboda likitocin ba su iya aiki yadda ya kamata a wannan yanayin na matsatsi.
Wannan yanayi na rashin asibiti ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, musamman ma mata masu juna biyu.
Akasarin matan suna mutuwa ne yayin da ake ƙoƙarin kai su asibiti a Minjibir ko Gezawa.
Wata mata a ƙauyen mai suna Zainab Abudullahi ta shaida wa BBC cewa ba ta jin dadi duk lokacin da ta kai yaronta wannan shagon da ake amfani da shi a matsayin asibiti.
Ta kuma ƙara da cewa ta rasa ƴaƴanta biyu sakamakon kwararar jini da suka samu yayin da suka je haihuwa.
”Cikin shekara biyun nan duk lokacin da na kawo ƴaƴana wannan wurin, bakin ciki ya kan lulluɓe ni ganin cewa shago ne mu ke amfani da shi a matsayin asibiti, saboda ko likitocin ma ba su jin daɗin yadda shagon ya ke saboda ƙanƙantarsa,” in ji Zainab.
Ta ƙara da cewa ”na rasa ƴaƴana biyu yayin da suke naƙuda. Wanda ya faru a baya-bayan nan, makonni kaɗan ne da suka gabata kuma bayan ta haihu ne sai jini ya fara zuba, muna hanyar kai ta babban asbitin Gezawa ta mutu.”
Zainab ta ci gaba da cewa ”ɗaya ɗiyar tawa da ta daɗe da mutuwa ita ma sakamakon zubar jini ne bayan haihuwa.”
”Da ace akwai asibitin ƙwarai a Baita, da ƴayana biyu na da rai har yanzu, saboda haka ina kira ga gwamnati da ta zo ta gyara mana asibitinmu,” in ji ta.
Haka kuma wani mzaunin yankin mai suna Rabi’u Abdulmuminu, ya ce shi ma ya rasa matarsa da jaririnsa sakamakon taɓarɓarewar ɓangaren kiwon lafiya a Baita.
”Mutane da dama sun rasa ƴan’uwansu kuma hakan ya faru da ni cikin watannin baya saboda na rasa matata da jaririna.”
Abdulmimunu ya ƙara da cewa ”lamarin ya faru ne da dare lokacin da matata ke ƙoƙarin haihuwa amma ta sha matuƙar wahala sakamakon rashin asibitin da mu ke fama da shi.”
”A lokacin da muka kai babban asibitin da ke Gezawa ƙarfinta ya riga ya ƙare, jaririn ya riga ya mutu a cikinta kafin ta kai ga haifarsa,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa ”daga baya ita ma ta zo ta rasu, kuma na san da cewa da muna da asibiti mai kyau da yanzu haka dukansu biyun suna raye.”
Hakimin Baita Alkasim Isiyaku ya ce sun yanke shawarar ficewa daga asibitin da suke amfani da shi ne saboda sun ga cewa ginin na iya rugujewa a kowanne lokaci sakamakon tsattsagewar da bangon ya yi.
Hakimin ya ce sun kwashe shekaru da dama suna aika wasiƙu zuwa ga gwamnati amma har yanzu ba ta mayar da wani martani ba.
”Mun kwashe shekaru muna rubuta wa gwamnati cewa muna buƙatar ta zo ta gyara mana asibitin amma har yanzu ba ta ce komai ba.”
Hakimin ya ƙara da cewa suna matuƙar miƙa godiya ga matar da ta yanke shawarar bayar da shagunanta domin su maye gurbin cibiyar lafiyar.
Hajiya Zuwaira Baita ta ce ta yanke shawarar bayar da shagunan ne kyauta saboda mata da yaran da ke bukatar ganin likita daga al’ummarta da kuma sauran ƙauyukan da ke kewaye da su.
”Ina ganin cewa mata da yara ba su iya ganin likita tun da cibiyar lafiyar da muke da ita ta daina aiki.”
Ta ce ”Mata masu juna biyu da dama daga ƙauyuka masu maƙwabtaka da jariransu sun dogara ne kan cibiyar lafiya ɗaya tilo da ke ƙauyenmu.”
”Sai na yanke shawarar bayar da gudunmawar shagunana na wucin gadi kafin gwamnati ta zo ta gyara mana namu asibitin.”
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati ta kawo masu ɗauki domin magance ƙalubalen da mata da yara ke fuskanta sakamakon rashin asibitin da ake fama da shi.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Abubakar Labaran Yusuf ya sahida wa BBC cewa ba shi da masaniya kan halin da ake ciki a Baita saboda bai samu wani rahoto a hukumance daga yankin ba.
”Ban samu wani saƙo a hukumance daga wurinsu ba, amma yanzu tun da na san halin da ake ciki zan tura mutane su je su ga yadda lamarin ya ke,” in ji shi.
”Zan duba in ga ko suna cikin ayyukan da muka shirya ƙaddamarwa, idan kuma ba su ciki zan yi ƙoƙarin sanya su cikin waɗanda za mu yi nan gaba a watannin farko na shekara mai zuwa.”
Labaran ya ƙara da cewa a halin da ake ciki yanzu akwai sama da cibiyoyin lafiya 2,000 a jihar kano.
Kuma an ma riga an zaɓi guda 11 daga cikinsu da za a yi wa garambawul.
BBCHAUSA