Dan Majalisar Wakilai Mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure RT Hon Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana nadin da Majalisar dattawa ta Najeriya tayiwa Sanatan Kano ta Kudu , Dist Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, a shugabancin kwamitin kula da hada hadar man fetur da Kasuwanci sa na majalisar da cewa an dora kwarya ne a gurbinta.
Alhassan Rurum yace matsayin Sanata Kawu Sumaila na jajirtacce akan duk Abinda ya sa gaba, Akwai yakinin zai yi kokari wajen Inganta bangaren harkar Man fetur da Kasuwancin man a kasarnan.
Dan majalisar ya yabawa Zauren Dattawan na kasa da suka kalli cancanta da dacewar da Sanatan ke da ita suka Kuma dora masa wannan aiki da babu shakka zai taimaka wajen magance matsalolin da suka dabaibaye Batun hada hada(Kasuwanci) na man fetur a Najeriya.
- Kotu Ta Dage Ci Gaba Da Sauraren Shaidu A Shari’ar Da Ake Zargin Matashin Da Ya Cinnawa Masallata Wuta A Kano.
- INEC Ta Gargadi Wadanda Ba Su Da Katin Zabe Su Kauracewa Rumfunan Zaben Gwamnan Ondo
RT Hon Kabiru Rurum, Ya Mika godiya ta musamman ga Shugaban Majalisar Dattawan ta kasa Sanata Godswill Akpabio, da mataimakinsa ,Sanata Barau Jibrin, da dukkanin ‘Yan Majalisar Dattawan na kasa bisa wannan nadi da sukaiwa Sanatan na Kano ta Kudu tare da fatan Allah ya bashi ikon sauke nauyin da aka dora masa..
Banda wannan kwamiti da Sanata Kawu Sumaila zai Kula dashi, Majalisar ta Kuma bashi shugabancin kwamitin wucin gadi da zai sanya ido a batun gyaran matatun man fetur na kasa…
*Fatihu Yusuf Bichi*
*Media Aide to RT Hon Kabiru Alhassan Rurum*
*Member Representing Rano, Kibiya and Bunkure Federal Constituency.*
*Chairman House of Representatives Committee on Airforce.*
*October 16th, 2024.*