Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu a majalisar dattawa, ya zargi ƴan siyasa, musamman ƴan majalisa da ƙarfafa shaye-shayen ƙwayoyi a tsakanin matasa.
Ya ce ƴan siyasa suna sayo wa matasan ƙwayoyi, sannan suna ƙarfafa musu gwiwar ta’ammuli da su domin samun damar yi musu dabar siyasa musamman a lokacin zaɓe, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kawu ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake nasa bayanin a kan ƙudurin da Sanata Rufa’i Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya ya gabatar, mai taken, “dokar kafa cibiyar hana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da gyara tunanin mashaya da sauran abubuwa masu alaƙa,” a yau Talata.
“Yanzu da nake wannan maganar, yawancin ofisoshinmu da gidajenmu ba za a rasa ƙwayoyi ba,” in ji Kawu.
“Na san wasu jagororin siyasa da suke ƙarfafa gwiwar masu shaye-shaye a Najeriya. Don haka akwai buƙatar mu ɗauki wannan batu da muhimmanci.”
Ya ƙara da cewa, “mutum nawa ne a cikinmu za su iya rantse wa Ƙur’ani ko Baibul cewa ba sa ƙarfafa wa masu shaye-shaye a mazaɓunsu?”
A ƙarshe ya yi kira da a riƙa yin gwajin shaye-shaye ga duk wani wanda yake son tsayawa takara.