Kenya na bincike kan wani ƙarfe da ya faɗo daga sararin samaniya

Spread the love
Kenya

Hukumomi a Kenya sun ƙaddamar da bincike kan wani ƙarfe mai nauyin kilogram 500 biyar da ya faɗo daga sararin samaniya a wani ƙauye da ke kudancin ƙasar a ranar Litinin.

Hukumar kula da sararin samaniya ta Kenya (KSA) ta ce abin da ya fado, ɓurɓushin wani ƙarfe ne da ke jikin na’urar harba kumbon sararin samaniya, kuma ta tabbatar wa mazauna yankin Makueni cewa ba shi da wani barazana ga tsaronsu.

Hukumar ta KSA ta ce ya kamata a ce ko dai ɓangaren kumbon ya ƙone, ko kuma ya faɗa wuraren da babu mutane, kamar teku.

Hukumar ta ƙara da cewa tana aiki, bisa ƙa’idojin duniya domin gane daga inda abin ya fito.

Dubban ɓangarorin nau’rorin da ake turawa sararin samaniya na faɗowa duniya a kullun, amma ba su cika zama barazana ga al’umma ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *