Kisan-kan da suka fi tayar da hankali a Arewacin Nijeriya .

Spread the love
Wadda ake zargi Hafsat Surajo

Kisan da ake zargin wata matar aure ta yi wa wani matashi a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya jawo ce-ce-ku-ce sakamakon yadda ake samun bayanai daban-daban da suke fitowa masu daure kai.

Tuni rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama Hafsat Surajo mai shekara 25 kan zargin kashe Nafiu Hafiz mai shekara 38.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya shaida Idongari.ng, cewa wadda ake zargin ta amsa laifin ta, inda ta tabbatar da cewa ta yi hakanne saboda shi yake hana ta kasha kanta.

Ta kara da cewa, kafin abun ya faruwa ta dauko wuka domin kashe kanta , amma yaron gidan nata ya hanata harma ya karbe wukar daga hannun ta.

Sai dai daga baya a lokacin da yake yin bacci ne ta caccaka masa wuka a sassan jikinsa kuma lokacin mijinta baya gidan sai dai ta fada masa abunda ya faru.

Marigayi Nafi’u

Sai dai wata majiya da ba a tabbatar da labarin ba ,na cewa hatta iyayen ta sun san tana fama da damuwa, ya yin da wasu kuma ke cewa har wajen magani an taba kaita sakamakon zargin cewar tana fama da Aljanu.

Kwamishinan yan sandan ya ce bayan binciken da suka gudanar, sun gano mijin matar mai suna Dayyabu Abdullahi mai shekaru 38 da kuma wani Mallam Adam, nada hannu a yunkurin binne marigayin ba tare da sanin yan uwansa ba.

Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta fara binciken masu ɓoye kayan abinci

Tubeless Photographer: Abba Al-Muatapha’s Censors Board and Tyrannical Impunity in the Guise of “Revenue Generation”

Mijin matar ya bayyana cewa, ya fara kiran yan uwan marigayin a waya da suke can jahar Bauchi inda ya fada musu  cewar ya rasu amma bai sanar da dasu musabbabin rasuwarsa ba.

Ya kara da cewa marigayin shi ne yake kular masa da wasu kayayyakin kasuwancin sa, sai dai mijin matar da ake zargi ya ce, matar tasa tasha furta masa kalaman kisan ko kuma ta yi yunkurin kashe kanta.

Mallam Adamu da ake zargi da yi wa Nafi’u wankan Gawa , ya shaida wa Idongari.ng cewa mijin matar ne, ya kira shi a waya har ya bayyana masa cewar, an yiwa marigayin aikin Basir amma ya mutu.

Hafsat, mijinta Dayyabu Abdullahi , Malam Adamu.

Ya kara da cewa bayan yaje gidan ne sai yaga jikinsa da alamun yankan wuka, bayan ya tambayi mijin matar , sai ya shaida masa cewa matarsa ce ta caccaka masa wuka.

Mallam Adamu ya ce, ganin abunda ya faru ne ya ce mu su ,ba zai iya ba,amma sai matar ta ce matukar ba iyi wankan ba zata kashe kanta, shi kuma ganin ta furta kalaman kisa ne yasa shi yin wankan.

Tuni dai dukkan wadanda ake zargi suka bayyana nadamar su, inda rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike zata gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Sai dai a tattaunawar da ‘yan jarida suka yi da mahaifin marigayi Nafiu, ya ce yana fata hukumomi za su dauki matakin da ya dace da kuma yin adalci don kada lamarin ya kasance kamar yadda wasu irinsa suka kasance a baya.

A kwanakin baya an samu irin wadannan lamura sau da dama a Nijeriya musamman a Jihar Kano, sai dai har yanzu babu wani kwakkwaran hukunci da aka zartar game da kashe-kashen da aka yi.

Maryam Sanda

A watan Nuwamban 2017 aka zargi Maryam Sanda da laifin kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello, wanda da ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP Halliru Bello.

Rahotanni a lokacin da lamarin ya faru sun ce Maryam ta samu sabani da mijin nata ne wanda hakan ya kai ga ta caka masa wuka.

Bayan faruwar lamarin aka gurfanar da Maryam a gaban kotu inda alkali ya yanke mata hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan samunta da laifin kashe mijinta.

Sai dai daga baya Maryam ta daukaka kara inda ta zargin alkalin kotun da shari’a bisa son rai. Har zuwa yanzu babu wani karin bayani game da ci gaban shari’ar Maryam.

Kisan Hanifa

 

Kisan Hanifa wadda yarinya ce mai shekara biyar a Kano ya yi matukar tayar da hankalin jama’a sakamakon yadda lamarin ya kasance mai ban tausayi da takaici.

Bayan kisan Hanifa, Babbar Kotun Kano ta yanke wa malaminta Abdulmalik Tanko hukuncin kisa bayan samunsa da laifin garkuwa da Hanifa da laifin kisanta da kuma laifin kitsa yadda za a yi garkuwa da ita.

Tun da farko malamin na su Hanifa ne ya hada kai da wasu domin sace ta inda daga baya ya kashe ta sannan ya binne ta a cikin wani buhu.

Sai dai tun bayan yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa, babu wani karin bayani game da aiwatar da hukuncin na kisa a kansa.

Ummita da Dan China

Frank Geng Quarong

A shekarar 2022 ne aka zargi wani dan kasar China mai suna Geng Quangron da kashe budurwarsa mai suna Ummulkulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.

Shi ma wannan lamarin ya tayar da kura wanda hakan ya sa aka shafe makonni ana tafka muhawara a shafukan sada zumunta.

A lokacin da lamarin ya faru, an zargi dan kasar Chinan da bin Ummita har gidansu da ke unguwar Janbulo inda ya soka mata wuka wanda hakan yayi ajalinta.

Daga baya an gurfanar da Mista Geng a gaban kotu inda ya amsa laifin kisan Ummita tare da cewa ya kashe mata kudi sama da naira miliyan 60.

Sai dai har yanzu kotu ba ta yanke hukunci game da wannan lamari ba.

Mahaifiyar da ta kashe ‘ya’yanta biyu a Kano

A watan Oktoban 2020 ne kuma aka shiga wani hali na ruɗu a birnin Kano, bayan da aka yi zargin wata uwa da kashe ƴaƴanta har biyu a Unguwar Sagagi.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yaran, Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da ‘yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekara uku.

A shekarar 2020 ne wani lamari mai kama da almara wanda ya matukar jawo ce-ce-ku-ce ya faru a unguwar Sagagi a Kano bayan wata mata ta kashe ‘ya’yanta biyu.

Ana zargin matar da kashe ‘ya’yanta biyu wadanda suka hada da Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da Zahra’u Ibrahim mai shekara uku bayan mijin ya yi barazanar yi mata kishiya.

Sai dai a bayanin da iyayen matar suka yi wa ‘yan sanda, sun ce ‘yarsu na da tabin hankali tsawon shekaru.

 

TUDUN BIRI A JAHAR KDUNA

Garin Tudun Biri

Tun bayan faruwar lamarin ne wanda sojoji suka sakowa masu taron Maulidi a garin Tudun Biri , ake ci gaba da nuna tsananin alhini,na yawan mutanen da suka mutu da kuma wadanda suka jikkata

Gwamnatin jihar Kaduna abunda ya faru na takaici ne matuka.

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna matukar damuwarsa, kuma ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Rigasa a karamar hukumar Igabi a jihar, a yayin wani hari na jirgi maras matuƙi mallakar sojojin Najeriya.

Lamarin da ya faru a lokacin da “sojin na Najeriya suka yi yunƙurin kai farmaki kan ƴan bindiga,” kamar yadda sojojin.

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan diyyar masu taron Mauludin da harin bom daga jirgin soja ya kashe a Jihar Kaduna.

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ne ya sanar da haka, sa’o’i kadan bayan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin.

Ministan ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro da Gwamnatin Kaduna za su yi aiki tare wajen gudanar da bincike kan abin da ya faru a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Harin dai ya auku ne a lokacin da wata makatar Islamiyya take gudanar da bikin Mauludi a daren Lahadi a kauyen Tudun Biri, inda ta karbi bakuncin mahalartar daga kauyukan da ke kusa da su.

Ana tsaka da taron ne wani jirgi mara matuki mallakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya yi mahalarta taron ruwan bama-bamai.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 85 a harin baya ga wasu 66 da suka samu raunuka.

 

TRT AFRIKA/Idongari.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *