Rundunar yan sandan jahar Kano ta gurfanar da Hafsat Surajo a gaban kotun majistiri mai namba 37 dake zaman ta a Yankaba, bisa zargin ta da aikata laifuka 2 da suka hada da kisan kai da kuma yunkurin kashe kanta.
Haka zalika rundunar ta gurfanar da mijinta mai suna Dayyabu Abdullahi da kuma wani Mallam Adamu mai shekaru 65 ,bisa tuhumar su da hada .baki da boye gaskiya wajen bayar da bayanan karya.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa (Bawahala) ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa idongari.ng, da yammacin ranar Laraba.
Idan dai ba a mantaba idongari.ng, ya ruwaito mu ku cewar kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel (Fada da Cikawa) ya bayar da umarnin cafke matar da ake zargi da hallaka Nafi’u Hafiz, a yankin unguwa uku a ranar 21 ga watan Disamba 2023, bayan ricikin da ya hada su a cikin gida.
Ana zargin Hafsat da yin amfani da wata ta daddaba wa mariyin a sassan jikinsa wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwar sa.
Binciken yan sanda na farko-farko ya kai ga kama mijin matar da kuma Mallam Adamu wadanda suka yi kokarin boye laifin kisan kan da aka aikata tare da bayar da bayan karya kan abinda ya faru na musabbabin mutuwar Nafi’u.
Tuni dai wadanda ake zargin suka amsa laifukan da ake tuhumar su da aikata wa.
Bayan karanto mata kunshin tuhumar da ake yi mata, ta amsa laifin , amma daga bisani ta musanta zargin.
Ɗaya daga cikin lauyoyin waɗanda ake tuhuma, Barrista Rabi’u Sidi, ya ce takardun kotu sun nuna cewa an tuhumi mijin Hafsat ne da wani malami da kuma ƙarin wani mutum da haɗa baki wajen ɓoye babban laifi da kuma bayar da bayanan ƙarya.
Shi ma wani, Barista I.S Abdullahi, lauyan malamin da ‘yan sanda suka kama bisa zargin yi wa mamacin wanka, ya ce wanda yake karewa ya musanta tuhume-tuhumen da aka yi masa.
Ya ce sun nemi kotu ta bayar da belin waɗanda ake ƙara, amma masu gabatar da ƙara sun nemi kotu ta ba su dama su yi nazarin wannan buƙata kafin bayar da matsayinsu.
Sai dai Kotun ta sanya ranar 8 ga watan janairu 2024 dan ci gaba da shari’a.