Kisan Nafi’u: Kotu ta yi umarnin a duba kwakwalwar Hafsat Chuchu bayan ta yi gum da bakin ta.

Spread the love

Shari’ar da ake zargin matar auren nan mai suna Hafsat Surajo (Chuchu), da zargin hallaka abokin kasuwancin ta Nafi’u Hafiz, a gaban babbar kotun jahar Kano mai namba 13 karkashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf, ta dauki wani sabon salo, bayan an karanto mata kunshin tuhumar har sau bakwai amma ta yi gum da bakin ta taki cewa komai.

Haka zalika an gurfanar da mijin Hafsat Surajo mai suna Dayyabu Abdullahi, Mallam Adamu Mohd da kuma Nasidi Muhammed, wadanda ake tuhuma da laifin boye gaskiyar abunda ya faru game da mutuwar Nafi’u, da bayar da bayanan karya, wanda yin hakan ya saba da sashi na 167 na kundin Penal Code.

An gano inda ake sayar da jarirai a Anambra

EFCC ta gayyaci shugabanin jami’o’in Najeriya da ake karbar kudin makaranatar da dala

Jaridar Idongari.ng, ta ruwato cewa, jami’in kotun Bashir Bello Fagge, ya karanto wa Hafsat Surajo kunshin tuhumar aikata laifin kisan kai ta hanyar caccaka wa Nafi’u wuka a sassan jikinsa, karkashin sashi na 221 na dokar kasa, har sau bakwai ana karanta mata inda ki yin Magana.

Da farko mai shari’a Zuwaira Yusuf , ta ce adan jinkirta sakamakon Hasat Surajo, ta yi gum da bakin ta ko wani abune ya hanata yin Magana,kuma bayan an dawo an sake karanta mata tuhumar , nan ma taki cewa komai.

Lauyar gwamnatin jahar Kano, Barista A’isha Mahmud, ta roki kotun akai wadda ake tuhumar ta farko asibiti domin a duba kwakwalwarta sakomakon kin cewa komai da ta yi.

‘’ Idan an samu irin hakan, wanda ake tuhuma ya yi shiru , a shari’a ana bayar da dama a duba kwakwalwar sa , zai iya yiwu wa ne,  ya yi hakan saboda keta ko kuma rashin lafiya’’A’isha Mahmud’’.

Sai dai koda aka karanto wa,Dayyabu Abdullahi, Adamu Mohd da kuma Nasidi Muhammed, kunshin zargin boye gaskiyar mutuwar Nafi’u da kuma bayar da bayan karya sun amsa da cewar sun fahimci abunda ake tuhumarsu.

Lauyan dake kare wadanda ake tuhuma na 1,2 da na 3 barista Haruna Magashi, ya bayyana cewa, wadda ake zargi ta farko taki yin maga domin ba ta ce Eh ko a a ba.

Idongari.ng facebook link https://www.facebook.com/profile.php?id=100089819831293

Barista Magashi ya kara da cewa bisa zargin ake yi ko suna da hannu wajen hana ta yin maga ya ce basu da hannu.

‘’ to shi dai abunda mutane suke ta zargi to ai hakki ne na mutum ya yi zargi, hakki ne ya dauki ra’ayin da yake so, amma kuma tabbatacciyar Magana kuma ta na da ahalinta dan haka yan jarida da kuke zuwa kotu kune za ku fada al’umma sashin abunda ya faru, idan akwai wani zargi ku shaida wa al’umma idan babu ku fada mu su’’ Barista Haruna Magashi’’.

Lauyoyin wadanda ake tuhuma 2,3 da na 4, sun nemi a bayar da belinsu, sai dai kotun ta jinkirta yin hukunci kan rokon beli ko akasin haka zuwa nan gaba.

Mai shari’a Zuwaira Yusuf , ta bayar da umarni ga likitan dake gidan gyaran hali da tarbiya na Goron Dutse , ya binciki lafiyar kwakwalwar Hafsat Surajo, sakamakon kin yin Magana bayan karanto mata kunshin tuhumar har sau bakwai.

IDONGARI.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *