Kisan Nafi’u: Rashin samun shawarwari daga ma’aikatar shari’a ya sanya an sake dage shari’ar mijin Hafsat Surajo da wasu mutane 2 a kano

Spread the love

Kotun majistiri mai namba 37, dake Yankaba Kano, ta sake tsare mijin matar nan Hafsat Surajo ,da wasu mutane biyu, bisa zarginsu da hada kai da boye laifi da kuma bayar da bayanan karya.

A zaman kotun na yau Litinin, Lauyar gwamnatin jahar Kano Barista Hafsat Adda’u Kutama, ta roki kotun ta sake ba su wata rana sakamakon rashin samun shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jahar Kano kamar yadda idongari.ng ya ruwaito.

Sai dai guda daga cikin lauyoyin dake kare mutanen ukun da ake zrgi Barista Rabi’u S. Abdullahi, ya roki kotun  ta bayar da belin wadanda ake tuhumar.

‘’ Daman tun a wancan zaman muka nemi beli amma lauyoyin gwamnati suka roki a basu wata rana, kuma an dawo yau amma shawarwarin basu samu ba, dan haka suka sake bukatar a basu wata rana’’ Rabiu S Abdulla’’.

Wadanda ake zargin sun hada da,  Dayyabu Abdullahi, Mallam Adamu da kuma wani mutum daya.

Ana dai zargin sun boye gaskiya kan musabbabin mutuwar Nafi’u Hafiz, abokin kasuwancin Hafsat Surajo da ake zargin ta yi amfani da wuka ,ta caccaka masa a sassan jikinsa wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Kotun ta sanya ranar 18 ga watan Janairu 2024 domin ci gaba da sauraren shari’ar mutanen uku.

A ranar 27 ga watan Disambar 2023 ne, Rundunar yan sandan jahar Kano ta gurfanar da Hafsat Surajo a gaban kotun majistiri mai namba 37,bisa zargin ta da aikata laifuka 2 da suka hada da kisan kai da kuma yunkurin kashe kanta.

Haka zalika rundunar ta gurfanar da mijinta mai suna Dayyabu Abdullahi, Mallam Adamu mai shekaru 65 da wani mutum daya ,bisa tuhumar su da hada baki da boye gaskiya da bayar da bayanan karya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *