Yau ce ranar da Babbar kotun jahar Kano mai namba 17, karkashin jagorancin mai shari’a, Sunusi Ado Ma’aji, ta sanya domin yanke hukunci kan shari’ar da ake yi wa Frank Geng Quarong, da ake zargi da hallaka tsohuwar budurwarsa mai suna Ummulkursum Sani Bahari wato (Ummita).
Idan ba a manta ba, Idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewar, dukkan bangarorin biyu sun gabatar da shaidunsu kan shari’ar, da kuma jawabansu na karshe.
Kisan Ummita: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci ga Frank Geng Quarong
Sai dai Kotun a wannan Rana ta Talata ta sanar da dage zaman yanke hukuncin kan shari’ar, zuwa nan da kwanaki Goma sakamakon wasu dalilai.
Tun a ranar 16 ga watan satumba 2022, ake zargin Frank Geng, ya caccaka wa Ummita wuka a wasu sassan jikin ta sakamakon wata sa’insa da ta hadu su, inda hakan ya yi sanadiyar rasuwarta.
Masu gabatar da karar sun gabatar sa shaidunsu guda 6, yayin da bangaren wanda ake kara suka gabatar da shaidu biyu.
A baya dai Frank Geng , ya shaida wa kotun cewar ba da niya ya hallaka tsohuwar budurwar ta sa ba.