Kisan Ummita: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci ga Frank Geng Quarong

Spread the love

Babbar kotun jahar Kano mai namba 17, karkashin jagorancin mai shari’a, Sunusi Ado Ma’aji, ta sanya ranar 12 ga watan Maris 2024, domin yanke hukunci kan shari’ar da ake yi wa Frank Geng Quarong, da ake zargi da hallaka tsohuwar budurwarsa mai suna Ummulkursum Sani Bahari wato (Ummita).

Idan ba a manta ba, Idongari.ng, ya ruwaito mu ku cewar, dukkan bangarorin biyu sun gabatar da shaidunsu kan shari’ar, da kuma jawabansu na karshe.

Tun a ranar 16 ga watan satumba 2022, ake zargin Frank Geng, ya caccaka wa Ummita wuka a wasu daga cikin sassan jikin ta sakamakon wata sa’insa da ta hadu su, inda hakan ya yi sanadiyar rasuwarta.

Masu gabatar da karar sun gabatar sa shaidunsu guda 6, yayin da bangaren wanda ake kara suka gabatar da shaidu biyu.

A baya dai Frank Geng , ya shaida wa kotun cewar ba da niya ya hallaka tsohuwar budurwar ta sa ba.

yanzu dai kallo ya koma sama zuwa ranar da kotun ta sanya dan yanke hukuncin , kan kisan Ummita , sakamakon zira idanu da al’umma suka yi kan shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *