Kisan Ummita: Wata babbar kotun jahar Kano ta sanya ranar sauraren jawaban karshe kan tuhumar da ake yi wa Frank Geng Guarong.

Spread the love

Babbar kotun jahar Kano mai namba 17 dake zamanta a unguwar Miller Road, ta dage ci gaba da sauraren shari’ar dan kasar Chaina, mai suna Frank Geng Quarong, da ake zargi da hallaka tsohuwar budurwarsa tun a ranar 16 ga watan satumba 2022.

A zaman kotun na ranar Litinin lauyan gwamnatin jahar Kano Barista Ibrahim Arif Garba, ya shaida wa kotun cewar lauyan , wanda ake tuhuma Barista Balarabe Muhammed Dan-Azumi bai basu jawabin karshe ba, akan lokaci sai a ranar 27 ga watan Disambar 2023, inda suke ci gaba da yin nazari akai.

Lauyan gwamnatin jahar Kanon, ya roki kotun ta ba su wata rana dan gabatar da jawabin karshe kamar yadda idongari.ng, ya ruwaito.

Lauyan wanda ake zargi Barista Balarabe Muhammed Dan-Azumi, ya shaida wa, idongari cewar ya bayar da rubutaccen jawabin karshen tare da hujjojin da yake neman kotun ta saki wanda ake zargi, bisa rashin kwararan hujojji da masu gabatar da kara suka gabatar cewar ya aikata laifin.

Mai shari’a Justice Sunusi Ado Ma’aji ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2024, dan bangarorin shari’ar su gabatar da jawaban su na karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *