Babbar kotun jahar Kano, ta yanke wa FrankGeng Quarong hukuncin kisa ta Hanyar rataya har sai ya mutu.
Tun a ranar 16 ga watan satumba 2022, Frank Geng, ya hallaka tsohuwar budurwarsa mai suna Ummulkursum Sani Buhari wato ummita a Unguwar jambulo Kano.
Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ya yanke masa hukuncin ne bayan gamsuwa, da hujjojin da Masu gabatar da Kara suka gabatar a agaban kotun.
A yanke wa Frank hukuncin ne karkashin sashi na 221b, Wanda ya yi daidai da hukuncin kisa.
Lauyan gwamnatin jahar Kano barista Haruna Isah Dederi , ya bayyana cewa alkalin kotun ya yi adalci wajen yanke hukuncin, sakamakon duk Wanda aka Samu da laifin aikata kisa to shima hukuncin kiss za a yanke masa.
Kotun dai ta ce za a rataye shi har sai ya daina motsi.
Mahaifyar Ummita, Hajiya Fatima Zubairu, ta bayyana farin cikin ta kan wannan hukuncin da kotun ta yanke wa Frank bisa hallaka yarta da ya yi.
A bangaren lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma barista Muhammed Dan-Azumi , ya ce za su dauka karara.
Yanzu haka dai al’umma musamman a jahar Kano, sun bayyana gamsuwarsu da hukuncin da kotun ta yanke.